Kafanonin sadarwa a Najeriya suna neman a kara kudin yin waya da kashi 40 cikin 100 sakamakon tashin farashin gudanar da kasuwanci a kasar da su ka ce ana fuskanta.
ABUJA, NAJERIYA —
Kamfanonin Sadarwar a karkashin Kungiyar Masu lasisin Sadarwa ta Najeriya ne suka aika da wannan shawara ga Hukumar Kula da Sadarwa ta kasa amma masu ruwa da tsaki na cewa Gwamnati ce ke da hurumin yin karin kudin waya ba Kungiyoyi ba
A takardar shawarar da Wadanan Kamfanonin sadarwa karkashin Kungiyar Masu Lasisin Sadarwa ta Najeriya suka aika wa Hukumar Sadarwa ta kasa wanda suka yi wa lakabi da Tsarin Tattalin Arziki da Tsaro a Bangaren Sadarwa, na son farashin layin waya ya tashi daga Naira 6.4 zuwa Naira 8.95 yayin da farashin sakon kar ta kwana wato sms ko text zai tashi daga Naira 4 zuwa Naira 5.61.
Kungiyoyin sun ce tabarbarewar tattalin arziki da cutar Korona ta kawo da kuma yakin Rasha da Kasar Yukurain ne suka haifar da hauhawar farashin makamashi da ya sa kudaden gudanar da ayyukan su ya hau da kashi 35 cikin 100.
Ku Duba Wannan Ma
Kamfanoni Biyu Na Salula A Najeriya Sun Yi Nasarar Samun Lasisin Fasahar 5G
Masanin harkar sadarwa mai zaman kansa a Abuja Auwal Abdullahi yayi karin haske akan hujjojin da kungiyoyin suka bayar. Bisa ga cewarsa, suna da kwararan hujjojin kara kudin wayar kasancewa farashin komi ya tashi sakamakon matsaloli da aka fuskanta da suka hada da barkewar annobar korona da ya haifar da tsadar kudin canji. Akwai kuma batun haraji da aka karawa kamfanonin wayoyin salulan, sai kuma tsadar man dizel. Yace wadannan duka na daga cikin hujjojin kamfanonin na neman kara kudin yin waya.
A hirar su da Muryar Amurka, wadansu masu amfani da wayar sadarwa sun bayyana takaicin su kan wannan shawarar, tare da yin kira ga hukumomi su yi watsi da wannan shirin da suka ce zai kara nawaitawa talakawa.
A nashi bayanin, masanin kundin tsarin mulki da shari'a Barista Mainasara Umar ya ce kungiyoyi basu da hurumin karin kudin waya
Shi ma shugaban hulda da manema labarai na Hukumar kula da Sadarwa Ike Adinde ya bayyana cewa Hukumar Sadarwa ta kasa ce kadai ke da hurumin kara kudin waya a Kasar.
Comments
Post a Comment