Yadda zaka Maida YouTube Video Zuwa GIF
Wasu mutane da dama idan suna kallon Video a YouTube sukan so su mayar da dan wani sashe ko yanki na Video Zuwa GIF. GIF dai kamar yadda kowa ya sani shine wani Dan karamin hoto mai motsi Mai kama da sticker, Dan dai ya dara sticker girma, ana amfani dashine a jikin keyboard wajen tura sakonni. To wannan Dan guntun hoto zaka ga Yana motsi kamar dai video dandai tsawon sa bai wuce 'yan sakanni. To a takaice shine GIF.
Zai iya kasancewa kana kallon Video dai dai Wani scene na Wani Jarumi da kake so ko wani abin dariya ko abin mamaki, ko ma dai meye to sai ka yanke dai dai wajen ka mayar dashi GIF, wato dan karamin hoto mai motsi, don turawa a duk wani messaging platforms. Platforms din da ke daukar GIFs sune irinsu WhatsApp, Telegram, Facebook da Kuma Instagram.
Lokutta da dama zaku ga wajen sending messages ko chat tura plain text baya gamsarwa har sai an hada da tura GIFs don nuna ma wanda kake maganar dashi yanayin da kake ciki. Shi wannan GIFs din amfaninsu shine zasu bayyana ma wanda kake magana dashi halin da kake ciki. Misalin bacin rai, ko mamaki, darin ciki da dai Sauran emotions na Dan Adam.
Ga Wanda yake son maida video Zuwa GIF zai download din duk Wani video da yake so daga YouTube, Zuwa kan computer dinsa sai ya shiga website da ake kira GIFs.com, sai ya yi turning Video to GIFs.
Idan zaka mayar da GIFs daga YouTube video, da farko zaka bude video a desktop dinka ta chrome browser idan ita kake amfani da ita, ko Kuma ko wace browser. Idan video ya bude, sai kaje saman browser din kai clicking sau biyu a URL, sai kayi edit kasa "gif" kusa da kalmar YouTube din misali "https//wwwyotube.com/example
Bayan ka dora wannan kalmar ta gif zai zama https;//www.gifyoutube.com/example bayan ka gama editing sai ka danna enter, sannan ka jira har web page din ya gama loading, so daga nan zaka ga ka koma GIFs.com, a nan ne zaka ga video dinka ta bangaren dama, da Kuma abubuwan editing a bangaren hagu.
To daga nan ne zaka zabi bangaren da kake so daga cikin video Wanda zaka mayar GIF a jikin editor din. Abu nagaba shine zaka jawo wato drag na part da ka zaba ko dai karshen part din sai kayi highlight in blue don daidaita tsawon GIF din.
Daga nan bayan kayi captioning dinshi yadda kake so sai ka danna button na create GIF daga sama wajen hannun dama na screen din. A nan zaka ga button din.
Comments
Post a Comment