Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ganin watan Shawwal, wanda ya kawo karshen watan azumin Ramadan a kasar.
Tuni dai Shugaba Mohamed Bazoum ya aike da sakon 'Barka da Sallah' ga ilahirin al'ummar kasar a shafinsa na Tuwita, inda ya yi addu'ar zaman lafiya da tsaro da hadin-kan kasar.
A tous les Nigériens, à toute la Umma islamique, je formule des voeux ardents d'une bonne fête de l'Aïd el Fitr dans la paix, la sécurité et la solidarité. Qu'Allah accepte nos dévotions et nos privations et qu'Il nous gratifie d'un bon hivernage. #MB
Wannan na zuwa bayan Najeriya, makwabciyar Nijar, ta sanar da cewa ba a ga watan ba tare da ayyana Litinin a matsayin ranar Sallah.
Kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi tare da hadin gwiwar kwamitin ganin wata na kasa ya ce bai samu wani rahoto daga kwamitoci daban-daban na kasar da ke tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal ba.
Sarkin Musulmin Najeriya dai ya yi wa al'ummar Musulmin Najeriya addu'a da fatan Allah Ya yi musu jagora.
Ya kuma bukace su da su ci gaba da yi wa kasa addu'ar zaman lafiya da ci gaba. Yana yi wa daukacin al'ummar musulmi barka da Sallah.
Haka kuma, wannan na zuwa ne yayin da wasu kasashen Musulmi na duniya da Saudiyya suka sanar da rashin ganin watan a ranar Asabar.
Comments
Post a Comment