Main menu

Pages

ALHMDLILLH, MUSULUNCI YAYI NASARA A JIHAR LAGOS

 



MUSULUNCI YAYI NASARA A JIHAR LAGOS


Yau juma'a babban kotun koli ta Nigeria (Supreme Court) kotun dake ke sai Allah Ya isa, ta yanke hukuncin bawa mata dalibai Musulmai a jihar Lagos 'yancin saka Hijabi a Makarantun Primary da Secondary



Manyan Lauyoyi masu shari'ah na Kotun Supreme Court guda 7 ne sukayi zama a yau suka tafka muhawara, guda daya ne a cikinsu yaki amince a bawa Musulmai 'yancin saka Hijabi, ga sunayen masu shari'ar:

1- Justice Olukayode Ariwoola

2- Justice Kudirat Kekere-Ekun

3- Justice John Inyang Okoro

4- Justice Uwani Aji

5- Justice Mohammed Garba

6- Justice Tijjani Abubakar

7- Justice Emmanuel Agim.



Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito labarin, a shekarar 2017 lokacin Gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode yaron Bola Ahmad Tinubu ya daukaka kara zuwa Kotun koli (Supreme Court) akan kiyayyar da yake yiwa Hijabi bayan da a shekarar 2016 Kotun daukaka kara (Court of Appeal) ta yanke hukuncin bawa mata Musulmai 'yancin saka Hijabi a Lagos a makarantat Primary da Secondary


الحمد لله

 Yau Allah Ya yi ikonSa, Kotun koli ta bada 'yancin a saka Hijabi a Lagos, yaron Tinubu Akinwumi Ambode duk da baya kan kujeran Gwamna yaji kunya


Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmai

Comments