Main menu

Pages

BABBAR DAMA TA SAMUN TALLAFIN KARATU A KASAR WAJE

 



Yadda za ku samu tallafin karatu kyauta a kasashen waje

Shugaban daliban Najeriya da ke nahiyar Turai, Muhammad Bashir Sa'idu, ya bayyanawa BBC Hausa hanyoyi da 'yan kasar da ke son samun tallafin karatu a kasashen Turai za su bi wajen samun tallafin.



Bashir ya ce a halin yanzu akwai guraben tallafin karatu na kasar Turkiyya kuma suna kira ga 'yan Najeriya su bincika domin kar a yi babu su.


Ya kuma ce akwai damarmakin karatu da yawa amma 'yan Najeriya ba su san da su ba.



Shugaban daliban ya kuma ce na farko shi ne mutum ya tabbatar duk takardunsa sun cika daidai.



"Mutum ya tabbatar adireshinsa na imel yana aiki kuma yana bincika shi a-kai-a-kai sannan ya cike takardunsa a wurare da aka tanadar domin yin hakan," in ji Bashir.



Ya kara da cewa idan dalibi ya samu tallafin karatu na kashi dari bisa dari za a dauke masa duk dawainiyar karatun.



"Za a ba ka kudin abinci dala dubu hudu sannan za a kama maka gida kusa da makaranta da kuma tikitin jirgi domin dawowa gida sau daya duk shekara a kyauta," a cewarsa.

Comments