Yanda zaka dawo da hotunan da ka rasa
Za ku iya dowo da hotunanku da suka goge a iPhone dinku, amma Wanda bai dade da gogewa ba, ko Kuma icloud backup.
Zaku iya dawo da hotunan da suka goge a cloud storage app irinsu Onedrive da Dropbox.
Idan har hotunan bacewa kawai sukai ba gogewa sukai ba to zaku iya gano su a boyayyar folder a photo app din.
Kamar yadda muka sani ne wasu mutane sun dauki hoto da Matukar muhimmanci da basa so su rasa ko guda a cikinsu.
To Koda ace mistakly ka goge hotunan ka to ga hanyoyin da Zaka dawo dasu.
Apple sun yo wani folder a cikin photo app da ake ce ma "recently deleted" wanda aikisu daya da recycle bin na computer dinka. Wannan folder zata ajiye hotunan da aka goge na tsawon kwana 30. a kwana na 31 abinda yake a recently deleted zai goge permanently but duk da haka akwai hanya mafi sauki da za ka dawo dasu.
Ga yadda zakai wajen dawo da su;
1. Zaka ka bude photo app
2. Zaka danna Albums dake jikin buttom menu, sai ka shiga "Albums"
3. Kayo scrolling kasa har sai kazo wajen Utilities section, sai ka danna Recently Deleted. Sai ka danna ka shiga
4. Sai ka danna Select dake sama bangaren dama na screen sai ka danna Recover. Shikenan zasu dawo.
Yadda zaka dawo da deleted photos daga backup.
Idan hotunan ka sun rigada sun goge daga recently deleted daga recently deleted folder, to Shima zaka iya dawo dasu ta hanyar restoring din wayarka daga backup din da akayi a baya.
To idan Kai hakan abubuwan ka zasu dawo
Comments
Post a Comment