Main menu

Pages

SABBIN DOKOKI GUDA 4 GA KAFAFEN SADA ZUMUNTA

 



Sabbin dokokin Federal Govement ga social media


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da wani daftarin dokoki ga kamfanonin shafukan sada zumunta na Tuwita da Facebook da WhatsApp da Instagram da Google da TikTok da sauransu kan ayyukansu a ƙasar.


Dokokin, waɗanda aka samar da su don sa ido a kan yadda shafukan sa da zumuntar ke aiki, sun bayyana cewa dole kowane kamfani da ke aiki a Najeriya ya samar da duk bayanansa.


Sannan dole ya taimaka wa duk wata hukuma ta gwamnati da abin da take buƙata da nufin aiwatar da bincike ko shawo matsalolin laifukan intanet ko kuma shigar da ƙara a kan laifi.


Gwamnatin tana kuma so shafukan sada zumuntar su kiyaye dokokin Najeriya kuma kar su yi duk wani abu ko wata kwaskwarima da za su yi katsalandan ga dokokin ƙasar.



Hukumar Ci gaban Fasahar Sadarwa ta Najeriya NITDA ce ta fitar da sababbin sharuɗɗan, sakamakon umarnin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar.




Me NITDA ta ce?

NITDA ta ce an samar da sabuwar dokar ne don kare haƙƙoƙin ƴan Najeriya da ma waɗanda ba ƴan Najeriyar ba da ke zama a ƙasar, tare da samar da dokoki na mu'amala a tsarin intanet na zamani.


Hukumar ta ƙara da cewa: "Abin da yake a bayyane shi ne cewa abubuwan da ake yi a waɗannan dandali na sa da zumunta suna da matuƙar tasiri a zamantakewar al'umma da harkokin tattalin arziki da rayuwa gaba ɗaya.


"A saboda haka, dokokin wani ƙoƙari ne na gyara mu'amala tsakanin kamfanonin sa da zumuntar da ƴan Najeriya don kowa ya amfana, a yayin da muke son samar da tsarin tattalin arziki na dijita."


NITDA ta ci gaba da cewa: "Sabuwar dokar ta kuma fitar da tsare-tsaren bai wa ƴan Najeriya kariya da tsaro da kiyaye walwalarsu a yayin da suke amfani da shafukan.


"Muna son a dinga bibiyar ayyukan da ake yi a shafukan da suka shafi sanya abubuwan da suka take doka ko masu cutarwa."


Sannan NITDA ta ce dokokin za su samar da wani tsari na haɗa hannu wajen ƙoƙarin kare ƴan Najeriya daga duk wani abu da zai cutar da su a intanet, kamar kalaman ƙiyayya da cin zarafi da kuma daƙile labaran ƙarya.



Gwamnatin ta ce duk wani kamfanin sada zumunta da ke aiki a ƙasar dole ya yi wasu abubuwa da suka haɗa da:


1. A yi gaggawar ɗaukar mataki idan an samu ƙorafi daga wani mai amfani da dandalin ko wata hukumar gwamnati kan duk wani abu da ya take doka a shafin.


Dole kamfanin ya amsa cewa ya samu saƙon ƙorafin kuma ya cire abin daga shafin cikin awa 24.



2. A yi gaggawar cire ko hana ganin ko toshe duk wani abu da aka wallafa mai nuna al'aurar mutum, ko tsiraicinsa ko saduwa ko bidiyo na ƙarya na kwaikwayon wani, ko na batsa, musamman a yanayin da aka yi hakan da nufin cin zarafi ko wulaƙanta wani.


Dole kamfanin ya amsa cewa ya samu saƙon ƙorafin kuma ya cire abin daga shafin cikin awa 24.


3. A bayyana sunan wanda ya ƙirƙiri da wallafa saƙon idan har aka buƙaci hakan bisa umarnin kotu.


Musamman idan har umarnin ya shafi don a kare ko gano ko bincike ko shigar da ƙara kan laifin da ya shafi taɓa darajar Najeriya, ko na zaman lafiya ko tsaro ko huldar diflomasiyya, ko kan abin da ya shafi cin zarafin yara da kuma fyaɗe.


4. Idan kuma har wanda ya fara ƙirƙirar saƙon ba a Najeriya yake ba, to wanda ya fara yaɗa saƙon a Najeriya shi za a ɗauka a matsayin wanda ya fara ƙirƙirarsa.


Dole su sanya ido sosai don tabbatar da cewa ba a wallafa wani abu da ya saɓa wa doka ba a dandalin nasu.


Idan kuma wani kamfani ya samu saƙo daga wani mai amfani da shi ko wata hukumar gwamnati cewa an wallafa wani abu da ya taka doka, to dole wannan kamfani ya cire saƙon gaba ɗaya.


NITDA ta ce sabbin dokokin, waɗanda a yanzu aka fitar da su ga al'umma, an tsara su ne da haɗin gwiwa tsakaninta da Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa ta Najeriya NCC, da Hukumar da ke sa ido kan Kafafen Yaɗa Labarai NBC.

Comments