Asteroids: ƙaton dutsen da ya wuce ta gaban duniyarmu ta Earth
Wannan zanen hoton na nuna yadda astiriyod ke wucewa ta gaban Earth - amma shi wannan dutse na 7335 (1989 JA) zai wuce ne a nisan da ya fi na hoton nan
A ranar Juma'a 27 ga watan Mayun 2022 ne aka bayyana cewa wani ƙatoton dutse zai wuce ta gaban duniyrmu ta Earth.
An sanya wa dutsen suna 7335 (1989 JA) sannan kuma tsawonsa ya fi mil ɗaya.
Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka Nasa ta ce dutsen na asteroid, shi ne mafi girma da ya zo wucewa ta kurkusa da Earh a wannan shekarar.
Sai dai hakan ba wani abin damuwa ba ne - zai wuce lami lafiya ta gaban duniyar tamu da nisan mil miliyan 2.5.
Tawagar da ke bayar da bayanai kan hakan da ke cibiyar binciken abubuwan da ke zuwa kusa da duniyar Earth ta Nasa - wacce ke bin diddigin duwatsun da ke yawo a sararin samaniya kamar irin su astiroyid da kwamet da ƙananan duniyoyi - ta ce dutsen astiroyid ɗin, wanda shi ne na farko da aka gano fiye da shekara 30 da suka wuce, zai bi ta gaban duniyar ne ranar Juma'a 27 ga watan Mayu.
Comments
Post a Comment