Abbwn da ya kmt ju sani gane da Wanda zai na Atiku Abubakar mataimaki
Dan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya sanar cewa ya zabi gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023.
Jam'iyyar PDP ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis bayan tantance ɗaukar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar a hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja.
Wani Kwamiti da PDP ta kafa ne ya zaɓi mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasar don mara wa ɗan takararta Atiku Abubakar baya a babban zabe mai zuwa a bara.
Bayan wannan sanarwar hankali ya koma kan sanin ko wane ne Ifeanyi Okowa?
Atiku ya zabi gwamnan Delta Okowa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP
'Haɗa ɗan takara da mataimaki Musulmai a Najeriya ya saba wa dokar kasa
Tarihin Arthur Ifeanyi Okowa
An haifi Arthur Ifeanyi Okowa ne a ranar 8 ga watan Yulin 1959 a garin Owa-Alero da ke karamar hukumar Ika North-East ta Jihar Delta.
Ya fara karatu a makarantar firamare ta Iroro a Owa-Alero kuma daga baya ya tafi shahararriyar makarantar nan ta Edo College a Benin City daga 1970 zuwa 1976, inda ya samu shaidar karatu kuma ya kasance dalibin da ya fi nuna hazaka a dukkan tsohuwar Jihar Bendel a 1976.
Daga baya ya tafi Jami'ar Ibadan domin karanta ilimin zama likita, kuma ya kammala karatunsa a 1981, a lokacin yana da shekara 22 da haihuwa.
Bayan ya kammala karatun jami'a, da aikin yi wa kasa hidima, Dakta Okowa ya fara aiki a matsayin likita a hukumar da ke kula da asibitoci ta tsohuwar Jihar Bendel, kafin daga baya ya koma aiki a asibitin Victory Medical Centre a 1986.
Daga baya ya bude wani reshen asibitin a Boji-Boji da ke garin Owa.
Okowa yana da mata daya mai suna Dame Edith Okowa da 'yaya biyu: Marilyn Okowa da Mildred Okowa.
Rayuwarsa ta siyasa
A farkon rayuwarsa ta siyasa, Okowa ya rike mukamin sakataren karamar hukumar Ika, kuma daga baya ya zama shugaban karamar hukumar Ika Nort-East daga 1991 zuwa 1993.
Ya taba zama shugaban jam'iyyar siyasa ta Grassroots Democratic Movement (GDM) a Jihar Delta, amma daga baya ya shiga jam'iyyar PDP a 1998, kuma ya taimaka wa tsohon gwamna James Ibori a yakin neman zaben da ya yi na zama gwamna tsakanin 1998 zuwa 1999.
An nada shi Kwamishinan Ayyukan Gona daga 1999 zuwa 2001, kuma an tura shi Ma'aikatar Raya Albarkatun Ruwa daga 2001 zuwa 2003, sannan ya tafi Ma'aikatar Lafiya daga 2003 zuwa 2006.
A 2007, Okowa ya ajiye mukaminsa na Kwamaishina domin ya tsaya takarar gwamnan Jihar Delta, sai dai bai yi nasara a zaben fitar da gwani ba. A watan Yunin 2007, an nada Ifeanyi Okowa a mukamin sakataren gwamnatin Jihar ta Delta.
A shekarar 2011, an zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Arewacin Jihar Delta.
A shekarar 2015, Mista Okowa ya cika burinsa na zama gwamnan Jihar Delta a karkashin jam'iyyar PDP bayan da aka zabe shi da kuri'u 724,680, an kuma rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayun 2015.
An sake zaben sa a 2019, inda ya samu galaba kan Great Ogoru na jam'iyyar APC da kuri'u 925,274.
Gwamna Ifeanyi Okowa ne ya kafa Jami'ar Jihar Delta a garinsu na Agbor, kuma ya kafa wata Jami'ar ta Kimiyya da Fasaha a Uzoro, da kuma Jami'ar Dennis Osadebey a garin Anwai duka a Jihar ta Delta.
Yadda ya zama dan takarar mataimakin Atiku Abubakar
Dan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ne ya sanar da sunan Ifeanyi Okowa a matsayin dan takarar da zai yi masa mataimaki a babban zaben 2023.
Atiku ya sanar da sunan Okowa ne bayan taron babban kwamitin gudanarwa na jam'iyyar da aka yi a Abuja a ranar Alhamis.
Tun da farko shugaban jam'iyyar PDP Iyorchia Ayu ya bayyana cewa jam'iyyar ta kafa wani kwamitin mutum 17 domin ya zabo mutumin da ya fi dacewa.
Ya kuma ce kwamitin ya mika wa Atiku Abubakar sunayen mutum uku domin ya zabi wanda ya fi kwanta masa a rai.
Atiku Abubakar ya zabi Ifeanyi Okowa, kamar yadda ya ce "domin yana da kwarewar da ake bukata ya rike mukamin shugaban Najeriya a duk lokacin da shugaban kasa baya nan".
Ya kuma ce dukkan 'yan takara ukun da aka mika masa sun cancanta, sai dai Okowa ya fi kwanta masa a rai.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 za a rantsar da sabon shugaban Najeriya bayan babban zaben da za a gudanar tsakanin dukkan 'yan takara daga jam'iyyun siyasar Najeriya, inda dan takarar da ya yi nasara da mataimakinsa za su karbi ragamar mulki daga gwamnatin Muhammadu Buhari wanda wa'adin mulkinsa zai kare a watan Mayun 2027.
Comments
Post a Comment