Karuwa Da Mata Ke Samu Wajen Haihuwa.
TEAR Wato matsalar kari da mata ke haduwa da ita bayan haihuwa yanayi ne dake zuwa bayan mace ta haihu. Tsaffin mata wadanda suka haihu da yawa zasu iya fahimtar sun samu kari a gabansu, amma mafi yawa yaran mata basu cika fahimtar hakan ba sai sun fara jin ko ganin wasu alamomi.
Daga karshe unguwan zoma da mata masu ansar haihuwa sunfi kowa fahimtar mace ta samu kari. SHIN WANNAN MATSALA MENENE MAGANINTA? Kafin sanin maganin matsalar ya kamata asan wadanne alamomi za'aji ko gani a fahimci akwai alamar kari ga mace?
1, Tafiya bude.
2. Fitar iska
3. Budewar gaba
5. Zazzalowar mahaifa arika ji ko tabota ma.
Wadannan sune alamomin da mace zata ji kafin dubuwa, ba'a daukan mataki ko yanke hukunci sai anje dakin haihuwa a buda a gani.
Maganin wannan matsalar shine a dinke mace babu dubara ko kanikanci. wanda a da tsoro ke sa ake barin mata da matsalar abunda za a iya daukan shekara 10 da matsalar matukar ba dinkin akai ba.
Comments
Post a Comment