Manufofin da yasa aka sauya akalar NNPC
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabon kamfanin mai na kasar wanda aka sauya wa fasali, inda a yanzu kamfanin na NNPC ya koma wani kamfanin kasuwanci mai zaman kansa.
An ƙaddamar da sabon kamfanin ne a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar a Abuja babban birnin ƙasar ranar Talata.
Shugaba Buhari ya fara ne da gode wa mahartar taron, wanda ya kira shi da ''mai ɗumbin tarihi''.
To amma akwai wasu tambayoyi da ƴan Najeriya za su so jin amsoshinsu kan wannan batu.
BBC Hausa ta amsa tambayoyin bakwai ta hanyar tuntuɓar masana da ƙwararru da kuma jawaban da gwamnatin ta yi.
Me hakan ke nufin?
jawabin da ya gabatar a wurin taron, Shugaba Buhari ya ce an mayar da kamfanin mai zaman kansa ne saboda inganta shi, don samar wa ƙasar makamashin da take buƙata.
Ya ƙara da cewa ''daga yanzu ƴan kasuwa za su samu ta cewa wajen gudanar da harkokin kamfanin na NNPC, zai kasance kamfani mai zaman kansa ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa a fadin duniya.
"Domin ci gaba da bunƙasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da haɓaka fannin makashi a fadin duniya.
''A yanzu doka ta ɗora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Najeriya wadataccen makamashin da take buƙata domin samun haɓakar tattalin arziki ta hanyar farfaɗo da wasu fannonin da ke buƙatar makashin," in ji shugaban Najeriyar.
Kamfanin ba kuma zai ci gaba da yin dogaro da tallafin gwamnati ba.
An kuma ɗora wa kamfanin na NNPC alhakin ganin ya tabbatar da cewa an samu sauƙi a ɓangaren makamashin ƙasar da kuma taimakawa wajen ganin tattalin arzikin Najeriya ya haɓaka domin samar wa duniya makamashi.
Mene ne alfanunsa ga ƴan Najeriya?
Wani masanin harkar man fetur a Najeriya, Farfesa Ahmad Isah Haruna, ya ce matsawar ba sauya salon gudanar da kamfanin aka yi ba, babu wani abu da zai sauya.
''Idan da za a ce za a fara gabatar da wasu manyan sauye-sauye musamman na gyara matatun da ake da su ta yadda jama'a za su riƙa samun fetur da kalanzir da gas da disel cikin sauƙi to da matakin zai taimaka, amma idan su ma ƴan kasuwar da aka miƙa wa ragama za su ci gaba da shigo da man ne daga waje suna ɗora riba a kai to lallai a iya cewa an yi ba a yi ba'' in ji masanin.
Ya ci gaba da cewa ''Lokacin da za a sayar da kamfanin lantarki na Najeriya haka aka yi ta cewa idan ya koma hannun ƴan kasuwa za su gabatar da sabbin tsare-tsare da za su sa a rika samun wuta, su ma su riƙa samun riba, amma yanzu an samu wutar?'' in ji Farfesa Ahmad Isah.
To sai dai ra'ayin Dakta Kailani Muhammad, shi ma masani a harkar man ya sha bamban, domin a ganinsa wannan tsari zai sa a samu sauƙi wajen wadata ƙasar da man fetur a farashi mai rahusa.
Ya ce hakan kuma zai jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje, wanda zai taimaka wajen samar wa 'yan Najeriya ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da ilimi da kiwon lafiya da hanyoyi da sauransu.
Ya kara da cewa sanya ƴan kasuwa wajen jan ragamar kamfanin zai kawo wa ƙasar alfanu ba kaɗan ba.
Gwamnati ta daina biyan tallafin man fetur?
A cewar masanin, kamfanin NNPC a yanzu ya zama mai zaman kansa don haka shi yake da alhakin gabatar da duk wani tsari da zai bi don samun riba, kuma gwamnati ba za ta ci gaba da biyan kudin tallafin mai ba.
Ya ci gaba da cewa ko da kudin man zai ƙaru sakamakon rashin biyan tallafi da gwamnati ke bayarwa a baya babu yadda za a yi, shi kamfanin ne zai nemi kudin a wajen wadanda yake sayarwa makamashi don cike wannan giɓi.
Ya ƙara da cewa ''Dama shi ya sa tun farko mutane da dama za su iya kallon wannan mataki a matsayin ƙoƙarin kaucewa biyan tallafin, da kuma kaucewa shafawa kanta baƙin fenti a wajen ƴan ƙasa a duk lokacin da ta ƙara kuɗin mai''.
Tsarin zai iya magance wahalar mai a Najeriya?
Injiniya Yabagi Sani, masani ne kan harkar mai a Najeriya, kuma ya shaida wa BBC Hausa cewa cefanar da kamfanin kadai ba zai kawo sauƙin wahalar mai da ake fuskanta a faɗin ƙasar ba.
Ya ce muddin gwamnati na son samun sauƙi a wajen wahalar man fetur, to sai dai ta sayar da matatun ƙasar.
"Idan ba haka ba ba wani sauyi da za a samu," a cewarsa.
Ya ƙara da cewa "ba sai gyaran matatun kasar kadai ba, ya kamata a sayar wa 'yan Najeriya ko wasu mutane da ke son harkokin man fetur, idan aka sayar musu sannan za a sami saukin wahalar man fetur a Najeriya."
Sai dai Farfesa Ahmad Isah ya ce babu wani ci gaba da hakan zai haifar, domin su ma ƴan kasuwar da aka miƙa wa tsayawa za su yi su nemi riba.
''Ana yin kasuwanci don tausayin wani ne?, babu yadda za a yi mai neman riba ka ce zai ji tausayin wani, sannan wani kamfani ne aka taɓa sayarwa a Najeriya da za a ce yau ga shi ya dawo yana taimaka wa ƴan ƙasa?; in ji shi.
Ta yaya hakan zai taimaka wajen inganta matatun man ƙasar?
Farfesa Ahmad Isah ya ce sayo mai daga waje ya fi sauƙin kashe kuɗi da samun gwaggwabar riba ga kamfani a kan kashe makudan kuɗi wajen gyara matatun mai da ake da su, don haka hanyar da su ma ƴan kasuwar za su runguma ke nan.
Ya ce da a ce ma tun farko an gindaya musu sharaɗin gyara matatun man ne kafin miƙa musu, da hakan zai sa dole su gyara.
Shi ma Injiniya Yabagi Sani ya ce cefanar da kamfanin kadai ba zai sa a samu ingancin matatun kasar ba har sai gwamnati ta tashi tsaye wajen kawar da cin hanci da rashawa.
"Idan ba a yi maganin cin hanci da rashawa ba, matatun ƙasar ba za su inganta ba saboda ba wani tasiri da zai kawo, domin ai mutanen da aka saka tun a baya su ne har yanzu ke gudanar da harkar kamfanin," ya ce.
"Ban ga wani ingantuwa da zai yi wa matatun kasar ba har sai an yi abin da ya kamata, da yanzu an ce an kawo mutane ne daga kamfanin Exon Mobil ko kamfanin Shell ko kuma kamfanin Total, to a sannan ne za a samu ingancin matatun kasar da zai sa man fetur ya wadata."
Masanin ya ce muddin ba wannan aka yi ba, ba wani sauyi da za a samu a bangaren matatun kasar.
Gwamnati ba ta da iko da kamfanin ke nan?
Kan wannan batu Farfesan ya ce ita gwamnati ta jawo 'yan kasuwa a jiki ne don su gudanar da kamfanin a matsayin mai zaman kansa ba wai ta sayar da shi ba ne, don haka har yanzu tana da iko da shi.
''Babu yadda za a ce gwamnati ba ta da iko da kamfaninta ba tare da ta sayar da shi ba, 'yan kasuwa su suke da ikon taka rawa a kamfani amma har yanzu kamfanin Najeriya ne na gwamnati," in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnati ba ta yi cikakken bayani a kan su wa ta sayar wa kamfanin ba, babu karin bayani a kan sauye sauyen da za a samu da manufofin da aka sanya a gaba.
''A halin da ake ciki ma'aikatan NNPC su din ne dai har yanzu a ciki, babu wani sauyin shugabanci, babu karin bayani a kan shin zai ci gaba da amsa sunan NNPC ne ma ko kuwa, akwai abubuwa da yawa da ya kamata a fito a yi bayani a kansu'' a cewar Farfesa Ahmad Isah.
Me ƴan kasuwar za su amfana da shi?
Ya ce yanzu su dama ƴan kasuwa kakarsu ta yanke saƙa, za su ci bulus, an sakar musu mara kamar yadda suka jima suna fata, yana mai cewa za su yanka wa jama'a duk farashin da suke so tunda su suke da wuƙa da nama.
Amma Injiniya Yabagi Sani na da ra'ayin cewa hakan zai bai wa 'yan kasuwa damar sayen hannun jari a cikin kamfanin na NNPC.
Ya ce wannan shi ne amfani kadai da cefanar da kamfanin zai yi wa 'yan kasuwar kasar, saboda ba wani sauyi na kirki da aka samu na mutanen da ke tafiyar da harkokin kamfanin.
Matashiya
Najeriya ce ƙasa mafi arzikin mai a Afirka, inda take haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 2,500,000 a kowace rana.
Hakan ya sa ta zama ƙasa ta shida a duniya mafi arzikin man.
Sai dai kuma matsalar cin hanci da rashawa da ƙarancin kayan aiki na shafar yanayin ayyukan haƙar man cikin shekara 60 da aka shafe ana yi
Comments
Post a Comment