YAJIN AIKIN ASUU: Bayan kasa cika masu alƙawari, Buhari ya yi wa malaman jami’o’i barazanar kowa ya koma aji
Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna damuwar cewa tsarin ilmi a ƙasar nan zai iya ɗaukar dogon lokaci a shiririce, ta yadda zai shafi iyalai da kuma ci gaban Najeriya nan gaba.
Buhari ya yi wannan jawabi ranar Litinin a cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Buhari, wato Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin ɗin.
“Shugaba Buhari wanda ya karɓi tawagar Gwamnonin APC, ‘Yan Majalisar APC da shugabannin jam’iyya a Daura, lokacin da su ka kai masa ziyarar gaisuwar Sallah, ya ce tuni wannan yajin aiki da malaman jami’o’i ke yi ta jefa iyayen ɗalibai da ɗaliban cikin ƙunci da damuwa matuƙa.”
Tsawon watanni huɗu kenan ASUU na yajin aiki, wanda ta zargi Gwamnatin Tarayya da ƙin cika alƙawarin yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin Tarayya ɗin da ASUU.
“Mu na fatan ASUU za ta tausaya wa jama’a ta yanke wannan yajin aiki, domin daɗewar na ƙara yi wa tsarin ilmi illa sosai. Maganar gaskiya yajin aiki fa ya isa haka nan, ɗalibai sun zaunu a gida. Don Allah ya haƙura kada ku lalata kyakkyawar rayuwar al’ummar da za ta wanzu nan gaba.”
Bayan alƙawurran da Gwamnatin Tarayya ta sha yi wa Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta biya buƙatun su domin su daina yajin aiki, a yau kuma gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da kuɗaɗen da za ta iya biya wa malaman jami’o’i buƙatun da suke nema ɗin.
Ministan Ƙwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka yayin da Gidan Talabijin na Channels ke hira da shi a ranar Alhamis.
Kafin tafiyar ASUU yajin aiki makonni biyu da suka gabata, ƙungiyar ta ce duk da alwashi da alƙawarin da gwamnatin tarayya ta ɗauka bayan masu shiga tsakani, har da shugabannin ɓangarorin addinai sun sa baki, har yau gwamnatin ba ta cika alkawari ko ɗaya ba.
Idan ba a manta ba kuma, bayan an shiga tsakani a cikin watan Janairu, ASUU ta ce “idan malaman jami’o’i su ka sake tafiya yajin aiki, to a tuhumi Buhari, shi ne bai cika alƙawari ba.
Babba daga cikin alƙawarin da har yau aka kasa cika wa ASUU shi ne wanda Gwamnatin Tarayya ta ɗauka a rubuce (MOU) cewa za ta aiwatar (MOA), kuma ta sa hannu tun a cikin 2009.
ASUU ta soki gwamnati da yi masu wasa da hankali wajen ƙin biyan alawus, sai kuma biyan wani alawus ɗin cikin cokali, wanda kamata ya yi a biya su cikin bokiti.
ASUU ta yi ƙemadagas wajen ƙin yarda a ci gaba da biyan su albashi a tsarin IPPS na ƙeƙe-da-ƙeƙe, inda suka ce kamata ya yi a riƙa biyan su a ƙarƙashin tsarin biyan albashi na UTAS, wanda gwamnati ta yi watsi da shi.
Yayin da ASUU ta ce ba za su koma aiki na, shi kuma Minista Ngige ya ce ana nan ana tattaunawa domin a cimma matsaya, su amince su janye yajin aikin.
“Jama’a su lura fa gwamnatin tarayya ta ɗauko hanyar cika alƙawarin da ta ɗauka, domin har ya ramto Naira biliyan 200 daga Asusun Hukumar TETFund ta bai wa malaman jami’o’i. Kuma wannan biyan kuɗaɗen ariyas ne tun daga 2016 har zuwa cikin wannan mulki na mu.” Inji Ngige.
“Alƙawarin da ake ja-in-ja a kan sa yanzu, tun na cikin 2016 zuwa 2017. To a gaskiya ba mu da kuɗin a yanzu, amma dai za mu san yadda za mu bubbuga mu nemo kuɗin domin mu farfaɗo da jami’o’in da farfaɗo da kayan aiki da gine-ginen da ke da buƙatar ingantawa.”
Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya sake ɗaukar alƙawarin cewa yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta fara tsawon mako guda kenan, zai kawo ƙarshe kafin ƙarshen wannan wata na Fabrairu.
Sai dai kuma ASUU ta yi masa kunnen-ƙashi, inda ta ce za su ci gaba da yajin aiki, tunda dai har yau ɗin nan Gwamnantin Tarayya ko alƙawari ɗaya gyan-gyan ba ta cika masu ba.
Yayin da Ngige ke bayani a ranar Talata, yayin da aka koma kan teburin tattaunawa, ya ce gwamnatin tarayya ta yi mamakin yadda ASUU ta sake rankayawa yajin aiki, duk kuwa da shiga tsakani da manyan masu ruwa da tsaki a ƙasar nan suka yi, cikin su kuwa har da manyan shugabannin addinai a ƙarƙashin ƙungiyar NIREC.
Duk da haka dai Minista Ngige ya shaida wa wakilan ASSU cewa, “ina tabbatar maku wannan taro da muka yi zai haifi ɗa mai ido.”
Rashin Cika Alƙawarin A Ɓangaren Gwamnatin Tarayya:
Idan ba a manta ba, tun a ranar 9 Ga Fabrairu PREMIUM TIMES Hausa ta buga kakabin da Kungiyar Malaman Jami’a ta yi, inda ta ce ‘laifin Buhari ne idan su ka sake tafiya yajin aiki’.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) Reshen Jihar Legas, ta yi kira ga ‘yan Najeriya su tunkari gwamnatin tarayya gar-da-gar a kan matsalar da ke damun jami’o’in gwamnati, waɗanda su ke tilasta tafiya yajin aiki.
ASUU ta ce ƙungiyar na tafiya yajin aiki ne sai bayan ta yi iyakar dukkan ƙoƙarin sadantawa, amma abin ya faskara.
Idan ba a manta ba, ASUU ta nemi mambobin ta su ware rana ɗaya domin wayar wa ‘yan Najeriya kai cewa su na ja-in-ja da gwamnati ne domin su ceto jami’o’in ƙasar nan daga durƙushewa.
ASUU ta ce har yau Gwamnatin Buhari ta ƙi cika alƙawarin da ta ɗauka cikin 2020, wanda ɗaukar alƙawarin ne ya sa ASUU ta janye yajin aikin da ya shafe watanni 9 su na yi.
A jawabin sa yayin taron ganawa da manema labarai a Jami’ar Legas da ke Akoka, a ranar Talata, Shugaban ASUU na Legas, Adelaja Odukoya, ya ce rashin cika alƙawarin da gwamnatin Buhari ta yi lokacin da ta lallashe su har suka janye yajin aikin watanni 9 cikin 2020, shi ne zai sake haddasa masu tafiya wani yajin aikin.
“Don haka a tuhumi Gwamnatin Tarayya, laifin ta ne na rashin cika alƙawari idan mu ka sake tafiya wani yajin aiki, wanda babu makawa sai mun tafi nan gaba kaɗan, kwanan nan.” Inji shi.
Cikin makon jiya ne Buhari da shugabannin addinai sun yi wa malaman jami’a magiya kada su tafi yajin aiki.
Shugaba Muhammadu Buhari ya roƙi Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) cewa Gwamnatin Tarayya za ta cika alƙawurran da ta ɗaukar masu, amma su yi wa Allah su yi wa Annabi kada su tafi yajin aiki.
Ya ce yajin aikin zai dagula zangon karatun ɗalibai. Buhari ya ce gwamnatin sa za ta ƙara danƙara maƙudan kuɗaɗe domin inganta tsarin ilmi.
Buhari ya yi wannan alƙawari a lokacin da ya karɓi baƙunci Ƙungiyar Shugabannin Addinai, a ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar da Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), Samson Ayekunle.
A ranar Juma’a ce dai ASUU ta zargi Gwamnatin Tarayya da cewa ba ta iya cika alƙawurran da ta ke ɗauka a baya, wa. Kan haka ne ASUU ta ce gwamnatin tarayya ta ƙware wajen iya faɗa-ba-cikawa.
Amma kuma da Buhari ke magana, ya ce duk al’ummar da ke fatan ci gaba da kuma alheri, ba za ta yi wasa da harkokin ilmi ba.
Daga nan Buhari ya jinjina wa ƙungiyar mai lakabi da NIREC kan shiga tsakanin da ta yi wajen kawo ƙarshen yajin aikin da ASUU suka shafe shekara ɗaya su na yi.
Kafin nan dai sai da Buhari ya karɓi baƙuncin Kwamitin 2022 Na Musamman Na Manyan ‘Yan Kasuwa, Siyasa, Kafafen Yaɗa Labarai da Shugabannin Kungiyoyin Sa-kai da Kare Haƙƙoƙi, inda ya shirya masu walimar cin abinci tare da shi.
A wurin walimar ce Buhari ya shaida masu cewa Gwamnatin 2023 za ta gaji ingantacciyar dimokraɗiyya da ƙarfafan hukumomin tsaro.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatin 2023 wadda za ta gaje shi, za ta gaji tattalin arzikin ƙasar da aka bunƙasa ta hanyar inganta harkokin noma a cikin ƙasa, ingantacciyar dimokraɗiyya da ƙarfafan hukumomin tsaron da aka farfaɗo da su.
Buhari ya yi wannan jawabi ne a wurin taron shekarar 2022 domin karrama Kwamitin Shugabannin Harkokin Kasuwanci, Siyasa, Kafafen Sadarwa da Kungiyoyin Kare Haƙƙi, Buhari ya ce ya na fata da kuma ƙoƙarin ganin ya bar kyakkyawan tarihin barin Najeriya a cikin halin bunƙasa da ci gaba da haɗin kai da zaman lafiya, tsawon shekaru 24 ba tare da an yi wa dimokraɗiyya karan-tsaye ba.
Buhari ya ce gwamnatin sa za ta kammala wa’adin ta a cikin karsashi na nagartar ta a shekarar karshen mulkin sa.
“Yanzu dai ina kan hanyar shiga shekara ta ƙarshen mulki na. Lokaci ne da na ke so na ga na ƙara kafa wa nasarorin da na samu ginshiƙai a tsawon shekaru bakwai da na yanzu. Kuma na ga ba bar Najeriya a matsayin dunƙulalliyar ƙasa mai zaman lafiya da albarka.
“‘Yan siyasar cikin ku su daina haƙilon hawa mulki ki muƙami kawai, su riƙa tunanin yadda za su yi amfani da muƙamin domin su kawo canji a cikin al’umma.
“Haka manyan ‘yan kasuwar ku maza da mata, su sani cewa akwai martaba sosai a cikin aikin gwamnati da yi wa ƙasa ayyukan inganta ƙasa.
“Babbar abin tambaya ita ce shin ta yaya za mu yi amfani da albarkatun kasuwancin mu mu bunƙasa ƙasar mu?”
“Idan za a lura na sha sukar manyan mu da manyan ‘yan bokon mu, saboda wasun mu sun sha nuna cewa ba mu iya jurewa mu daina nuna ra’ayin son rai, bambancin siyasa da ƙabilanci da addinnanci a lokacin da buƙatar haɗin kai don ci gaban ƙasar mu ya taso.”
“Sannan kuma a cikin shugabannin mu da manyan mu akwai waɗanda su dai su ci riba kaɗai su ka sani, ita ce babbar buƙatar su a kowace harka.”
Buhari ya gode wa kwamitin saboda irin yadda ya kauda kai daga ririta ƙabilanci da addinanci.
Yayin da Gwamna Kayode Fayemi ke magana, gwamnan na Ekiti ya nuna damuwar sa kan afkuwar juyin mulki a wasu ƙasashen Afrika, Buhari ya ce to shi dai alfaharin da ya ke yi, shi ne a yanzu dai Najeriya ta wuce wannan batun, juyin mulki ya zama tarihi a Najeriya.
Comments
Post a Comment