Main menu

Pages

 



Falalar Sada Zumunci a addinance

Daga Abi Huraira (RA) ya ce: Wani mutum yazo wajen Manzon Allah (SAW) ya ce: Ya Manzon Allah Ina da 'yan uwa makusanta ina sadar da zumuncinsu suna yanke min, ina kyautata musu suna bata min, suna min wauta ina hakuri akan hakan. Sai Manzon Allah yace: In dai yadda ka fada hakane to kamar kana jefa musu garwashi ne a baki, kuma ba zaka gushe ba har sai Allah ya taimake ka akansu mutukar ka dawwama akan yadda kake. [Adabul Mufrad].



Daga Abu Ayyubal Ansary (RA) ya ce: Wani baqauye yazo wa Annabi (SAW) acikin wata tafiyarsa sai baqauyen yace: Fada min abinda zai kusantar dani ga Aljanna kuma ya nesantar dani daga wuta? Sai Manzon Allah ya ce: Ka bautawa Allah kada kayi shirka dashi da wani abu, kuma ka tsaida sallah, kuma ka bada zakkah, kuma ka sada zumunci. [Adabul Mufrad Hadis 49]



Abdurrahman bn Auff (RA) yana cewa yaji Manzon Allah (SAW) yana cewa: Allah (SWT) yace: "Nine Mai Rahama! Kuma nina halicci zumunci, kuma na tsago sunan zumunci daga sunana, duk wanda ya sadar da zumunci zan sadar dashi, kuma duk wanda ya yanke zumunci zan yanke shi".



Dukkanin wadannan hadisai na Manzon Allah (SAW) suna nuna mana falala ne dake cikin sadarda zumunci, don haka sai mu dage. 

Allah ya bamu ikon sadarda zumuncin mu.

Comments