Yadda Ake Hada hadadden Suya (Tsire) A gida
INGREDIENTS:
Nama,
borkono,
kuli-kuli,
citta,
kimba,
kanunfari,
masoro,
thyme,
curry,
busashen tafarnuwa
da sauran spices.
Mangyada,
gishiri,
maggi sai tsinkin tsire.
.
PROCEDURE:
Ki daka dukkanin spices naki tare da kuli, amma kulin ya ďan fi yawa, kuma ki sanya maggi da gishiri. A zabi nama mai kyau wanda babu kitse sosai a jiki, sai ki yanka shi sirara ta kwance da dan tsayi kadan sai ki ďauko tsinken tseren ki jera wannan naman a jiki.
Wato in kin huda ta ciki sai ki fitar da shi ta waje. Daga nan sai ki sami kwano ki zuba mangyada dai-dai misali tare da gishiri da maggi kaďan ki shafe jikin naman duka. Kina yi kina sanya shi cikin haďin kulin ya kama jikinsa da kyau. Daga nan in a oven ne sai ki yi ta jera su suna gasuwa. In ma a rushi ne duka ba damuwa.
Comments
Post a Comment