Yadda Ake Alalan Kwai Cikin Kwai
Abubuwan hadawa
Kwai
Attarugu
Albasa
Man girki
Maggi
Leda
Yanda ake hadawa
Da farko zaki sami kwanki ki fasashi a kwanan ki mai kyau ki kadashi Sai ki zuba kayan hadinki: attarugu, da albasa wanda dama kin yi giretin nasu da sauran kayan dandano dai dai misali Sai ki dunga zuba kwan naki acikin leda kina yi masa kamar kullin alalan leda Sannan sai ki dora ruwanki cikin tukunya ki dafa kullallen kwan naki
Idan ya dahu sai ki kara fasa wani kwai, kuma ki cire wannan kwan naki na leda kina yankashi yankan tsakiya za kiga ya bada shef din zuciya, watau ‘heart’ sai ki dunga tsomashi acikin wannan kwan naki Sai kuma ki soyashi a manki mai zafi sosai, amma ki yi suyar sama-sama don ya yi suya mai kyau
A ci dadi lafiya. Na gode.
Comments
Post a Comment