Main menu

Pages

TOFA! RIKICI TSAKANIN QUNGIYAR SSANU DA GWAMNATI AKAN ASUU

 


Kungiyar SSANU tace ba zata aminta da fifita Kungiyar ASUU akan su ba

Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a ta Ƙasa (SSANU), ta bayyana cewa za ta hau sama su rufto ƙasa su da gwamnatin tarayya, matsawar aka bambanta ko aka fifita albashin malaman jami’o’i (ASUU), fiye da na manyan Ma’aikatan jami’o’i (SSANU).


Shugaban SSANU na Ƙasa Mohammed Ibrahim ya ce sun yi mamaki da shiga firgici, jin cewa Kwamitin Daidaita Albashin malamai da ma’aikatan jami’a wanda Farfesa Nimi Briggs ke shugabanta, sun gana da ASUU har sun amince za a ƙara wa malaman jami’o’i tsakanin kashi 108 zuwa 180 na albashin su. Su kuma SSANU za a yi masu ƙarin cikin cokali na kashi 10 kacal.


Ibrahim ya ce kul aka kuskura aka yi haka, to gwamnatin tarayya ta jangwalo wani sabon rikici kenan, wanda ba a san ranar kawo ƙarshen sa a kotu ba.


Ya ce kwamitin Briggs ya gana da SSANU sau biyu kacal, amma kuma abin mamaki ya gana da ASSU fiye da sau 10.


“A iya zama biyu da kwamitin Briggs ya yi da SSANU, ba mu ma kai ga cimma matsaya ko yarjejeniya ga ƙarin albashin da za a yi mana ba.


“Amma mu na da masaniya sau fiye da 10 su na zama da ASUU. Don haka a yi mana ƙarin cikin cokali, rainin wayau ne. Idan hakan ya tabbata kuwa, za mu ruƙume a kotu mu da gwamnatin tarayya.” Inji Ibrahim.


Wannan fushi na SSANU ya biyo bayan wani rahoto da NAN ta buga wanda ya nuna cewa kwamitin Briggs ya amince a yi wa ASUU ƙarin kashi 108 zuwa 180, su kuma SSANU a yi masu ƙarin kashi 10 kacal.


SSANU ta ce an kafa kwamitin Briggs ne don a gyara matsalar da aka samar tun cikin 2009, ba wai don kwamitin ya ƙara dagula al’amurran ba.


SSANU ta ce ba ta yarda a fifita ASUU wajen karɓar albashi ba.


“Don an samu bambancin alawus wannan ba wani abu ba ne. Amma dai yayin da ASUU ke koyar da ilmi, SSANU kuma su ne ke kula da ɗaliban da halayyar su da ɗora su kan turba.


A ɓangaren rikicin ASUU da Gwamnatin Tarayya kuma, Shugaba Buhari ya umarci Minista Ngige ya tsame hannun sa daga tattaunawa da ASUU.


Tura ta kai bango a tirka-tirkar yajin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa da Gwamnatin Tarayya, inda har Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya tsame hannun sa daga jagorantar zaman sulhu da ASUU.


Buhari ya bayar da wannan umarni ne a ranar Talata, lokacin da ya gana da shugabannin ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin da yajin aikin malaman jami’o’i ya shafa.


An yi taron a Fadar Shugaban Ƙasa, inda nan take Buhari ya ce Ministan Ilmi Adamu Adamu ya karɓi ragamar jagorancin tattaunawa da zaman sulhu da ASUU, maimakon Minista Ngige.


A wurin taron, Adamu ya yi ƙorafi da kuma bayyana dalilin da ya sa tsawon lokaci sosai ba a jin ya na cewa komai dangane da yajin aikin malaman jami’o’i, duk kuwa da cewa shi ne Ministan Ilmi, ba Ngige ba.


“Tun cikin 2016 Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya ce aikin zaman sulhu da ASUU ba na Ministan Ilmi ba ne, na Ministan Ƙwadago ne.” Haka aka ce Adamu ya furta a wurin taron, inda ya ƙara da cewa bai manta ba bayan Ngige ya faɗa masa, har hujjoji ya gabatar daga cikin dokokin Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ma’aikata ta Duniya (ILO).


Ita ma ASUU ko a wani taron manema labarai da ta yi kwanan nan, ta zargi Ngige da kasancewa mutumin da ke kawo tsauraran matakan sasantawa, waɗanda hakan ne ke sa ASUU ɗin yi masa kunnen-uwar-shegu ta ƙi sasantawa da shi. ASUU ta ce Ngige ya janyo har aka kai zuwa yanzu ana yajin aiki.


Wata majiyar da aka yi taron da ita, kuma ya nemi a sakaya sunan ta, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Buhari ya umarci Adamu Adamu ya karɓi jagorancin zaman sulhu da ASUU, amma fa bai bai wa Ministan makonni biyu ba kamar yadda aka buga a jaridu a ranar Talata. Ya ce Adamu ne da kan sa ya sanar wa manema labarai cewa ya na ganin a cikin makonni biyu zai warware rikicin.


“Amma gaskiya Adamu bai ce zai magance rikicin cikin makonni biyu ba. Ya dai faɗa a wurin taron cewa, “Cikin 2016 a wurin taron Ministoci da Buhari a wannan lokacin Ngige ya furta cewa aikin zaman sulhu da masu yajin aiki ba aikin Ministan Ilmi ba ne, aikin Ma’aikatar Ƙwadago da Kula da Ma’aikata.


“A lokacin dukkan Ministocin da ke wurin babu wanda ya yi magana. Shi ma Shugaba Buhari bai ce komai ba. Don haka ganin ministoci ba su yi jayayya da Ngige ba, kuma shi ma Buhari ya yi shiru, sai Minista Adamu ya ga cewa duk ana goyon bayan Ngige kenan, har da Buhari kan sa. Dalili kenan ya kame bakin sa ya yi shiru, kuma a bar Ngige da gaganiyar sulhu da ASUU.” 

Comments