Main menu

Pages

YADDA AKE HADA INGANTACCEN TURAREN WUTA MAI DADIN KAMSHI

 


Yadda ake turaren wuta ingantacce


Turaren wuta ana yin sa ne da itace, domin turara daki, da dukkanin jiki da na tsugunno, da kuma na sutura . Ana zuba shi cikin gaushi ne a kasko. Nan da nan kuwa ka ji kamshi ya gauraye ko ina acikin gida. Daga cikin Itatuwa da ake turare da su kuwa Sun hada da :

Icce Sandal

Icce Hawi

Icce Gab-Gab

Icce Durot

Da dai Sauransu.


Ana yin turare na soyawa Kuma ana yin na jikawa. Ya Danganta Da bukata mutum.


Larabawa da kuma mutane Mai duguri ne su ka fi shahara wajen amfani da turare wuta. Mazansu na taimakawa sosai, siyawa matansu turare akai-akai. A wajensu tamkar dole ne amfani da turare . Mace ba ta Da daraja sai da kasancewa cikin kamshi akodayaushe .


Kayan Hadawa

Iccen Hawi

Matan Arewa

Farce

Misik

Madara turare ( 8)


Yadda Ake Hadawa


Za’a sa iccen Hawi a turmi a daddaka shi sama-sama. Asa iccen gab-gab shima haka. Sai a juye su cikin mazubi. A dauko ruwan turare Matan Arewa a zuba akan itatuwa. A juye Soyayye farce. A zuba Misik. Sai adauko turaruka : Alhaji Abdullahi, da salamalekum, da Sasorabia, da 20 fragrances. Kowanne a bude a juye. Sai Kuma a dauko Madara turare masu matukar kamshi a zuba su.

A juya da kyau ko ina ya samu ya hade . A samu mazubi ajuye aciki. Kuma arufe shi sosai.


Turaren Sukari

Ruwan turare ( alcohol)

Yara-yara gwangwani 1

Sikari kwano

Kala

Filabo

Madarori Turare 5


Yadda Ake Hadawa

A juye Sikari acikin mazubi. A juye Yara-yara, a sa madarori turare 5. Sai asa kala ayi ta juyawa har sai ko ina ya hade jikinsa sosai.


Shima wannan turare acikin gaushi ake sawa a turara daki da shi .


A karshe dai amfani da turare ya kewaye dukkan kasashe. Haka kuma da sauran jihohi. Ya Kuma cancanci ace yana ciki kasafin wata-wata na kowanne Mai gida. Gidanka kamshi Kuma jikin matarka kamshi. Haka zai sa ma Ma’aurata natsuwa da samu gamsuwa da juna. Duba yadda ake hadaddiyar humra .

Comments