Main menu

Pages

YADDA WANI YA ZABI SANA'AR WASAN WUTA




Yadda Sana'ar wasan Wuta ya karbi Wani matashi

 Sana’ar Solomon John Ebikeseye, matashi mai shekaru 26 da ake yi wa lakabi da Mai Wuta, kamar yadda ya bayyana ita ce "cin wuta, da kuma wasa da wuta."



"Wasu masu fasahar nishadantarwa sun zo don su gana da ni a gidana a shekarar 2017, inda suka bayyana min cewa suna neman mutumin da zai iya daukar wuta ya yi wasa da ita, ko ni zan iya yi?"



John ya shaida wa BBC Pidgin yadda aka yi ya fara sana’ar wasan wuta a shekarar 2017, a garinsa da ke jihar Bayelsa a kudancin Najeriya.



"Na rika tunani game da batun. Bayan da suka tafi, na dauki itace a bayan gidana, na daure shi da tsumma, sai na cinna wuta na fara wasa da ita.


"Da dare sai suka zo suka same ni suka ce, mun shirya fara wasan, sai na ce musu mu tafi kawai. 



Mun je wurin wasan, na kunna wutar, a yayin da suke tsakiyar wasan, ni kaina ina wasa da wutar, sai na ga taron jama’a na ta ihu suna jinjina wa wasan wutar tawa.


"Sai na ce ashe haka wannan abu ke birge mutane? Abin ya ƙara min ƙarfin gwiwa’’.



Ba rufa ido ko tsafi ba ne'

Ba a cika samun irin wannan fasahar wasan wuta a Najeriya ba, kuma hakan ne ya ƙara jan hankulan mutane.


John ya bayyana kalubale game da yadda mutane suka yi amanna cewa wasan gaskiya ne ba rufa ido ba ne ko kuma tsafi.


"Ba rufa ido ba ne, tsabar horo ne da ƙwarewa da nake yi a kullum a cikin gida.


"Wannan wasan wuta na da matukar hadari da kuma bukatar tsananin kuzari.


"A wasu lokuta na kan ƙona hannu da jikina, amma ina ƙara yi ina kuma ƙara yin taka-tsan-tsan."




Da farkon fari, John ya ce ya fuskanci ƙyama daga jama’a da ba su amince da sana’arsa ba, da waɗanda ke tsoro har sai da suka fahimta daga baya.


"Lokacin da na fara cin wuta, mutane sun yi watsi da ni sosai, a wasu lokuta idan na je yin wasa mutane kan fice daga wurin taron suna cewa shin mene ne wannan?


"Suna tsoron ka da wannan abin ya kƙna mu, kana mutane ba sa dauka ta a matsayin dan adam saboda suna ganin bai kamata mutane su riƙa wasa da wuta ba kamar yadda nake yi," ya bayyana.


'Zan iya amfani da wuta in yi komai’

Da farkon fari, John ya ce ya fuskanci ƙyama daga jama’a da ba su amince da sana’arsa ba, da waɗanda ke tsoro har sai da suka fahimta daga baya.



"Lokacin da na fara cin wuta, mutane sun yi watsi da ni sosai, a wasu lokuta idan na je yin wasa mutane kan fice daga wurin taron suna cewa shin mene ne wannan?


"Suna tsoron ka da wannan abin ya kƙna mu, kana mutane ba sa dauka ta a matsayin dan adam saboda suna ganin bai kamata mutane su riƙa wasa da wuta ba kamar yadda nake yi," ya bayyana.



Duk da cewa ina son wuta kuma ina haska dandamali da irin fasahata, masu wasa da wuta na Afirka na gargadi ga mutane da masu kaunarsu cewa sanaa’ar nada hadarin gaske kuma ba a wasa da ita yadda aka gad ama.


 


"Ba wai don ina wasan wuta ba ne, bay ana nufin cewa ku j uku gwada wasan wuta a cikin gidajenku ba ne, ina rokon ku kada ku gwada a cikin gida, shafe tsawon sa’oi da nake yi ina horar da kai na ne ya kai ni da wannan matsayi a yau." E tok.


 


John ya kuma yi magana game da illolin zabin da ya yin a sana’arsa.


Solomon John yana mai babban gargadi ga mutanen da ke da sha’awar gwada wasan wutar da cewa kada su gwada a cikin gida, amma su rika bin wanda yak ware don kaucewa hadari ko samun rauni


Ya kuma kara da cewa duk da cewa daya daga cikin kalubalen da yake fuskanta nan una rashin amincewa da sana’arsa a lokacin da ya fara, yanzu mutane sun fara amincewa da shi.


 


Yanzu haka, yana yin wasa a tarukan bukin murna cika shekara, da wiuraren shakatawa da sauran taruka, har ma da faya fayen bidiyon wakoki.




Comments