Main menu

Pages

AMFANIN SASSAKEN BISHIYAR GAMJI.

 



Amfanin sassaken Gamji ga lafiyarmu

Assalamu alaikum Warahmatullah

A yau zamuyi bayani akan amfanin da sassaken iccen Gamji keyi a lafiyarmu, kamar yadda muka sani ne cewa a duk Wani tsiri da Allah Ya tsirar a doron kasa to fa yana da amfani Kuma maganine, sai dai in mutum bai sani bako Kuma ilmin hakan bai iso gareshi ba.


Don haka a yau muka zo maku da amfanin iccen Gamji .


Ana tafasa sassaken Gamji ko a jika shi, shi kadai, a dinga sha don magance cututtuka da kuma kyautata lafiyar jiki. Ana kuma kiran bishiyar Gamji da suna Danko. A turance kuma ana kiransa 'Flake rubber tree'. 



1- Shan ruwan sassaken Gamji, wanda aka jika ko aka dafa yana karawa mutum yanayin jiki mai kyau. Wato ka ga jikin mutum ya yi sumul-sumul, ya kara kyan gani. 


2- Gamji na kara yawan ruwan nono, ga mata, masu shayarwa. 


3- Yana maganin ciwon ciki. 


4- Gamji babban sinadari ne mai matukar kara yawan jini ajikin mutum. 


5- Yana maganin gudawa. 


6- Yana magance matsalolin cikin ciki. 


7- Yana magance matsalar shafar Aljanu.


Don haka sai a samu sassaken iccen Gamji a tafasa ko a jika a dinga Sha domin samun wadannan abubuwa da aka zayyano.

Allah Ya sa a dace da Alkhairi Ameen.

Comments