Maganin ciwon Mara da wanke Mahaifa
Ga matar da take fama da ciwon mara musamman lokacin al'ada, ko idan zai zo yana zuwa da ciwon mara, wata ma zakaga hattana birgima a kasa, ko taji kamar ana soka mata wuka, ko rikicewar haila, ko jinin ya rinka zuwa da wari, ko karni, ko baki, ko yana zuba sosai to sai a samu: garin gwaiba rumzali na asali lemun tsami ruwa lita biyar (5lrt) sai a dafasu a rinka sha karamin kofi sau biyu (2) a rana za a'samu nasara insha Allah.
Domin tsabtace Mahaifa.
Ga mai bukatar tsaftace mahaifarta da kuma karramata da kashe duk cuta ko kwayar cuta dake zama bakin mahaifa, to wannan hadin da zamu yi bayani yanada muhimmanci musamman ga mai zafin mahaifa, ko kuma yara suna mutuwa a ciki, ko mai fama da toshewar bakin mahaifa ko kuma matsalar ta farune sakamakon amfani da wadansu magunguna na hana daukar ciki ba bisa ka'idaba, ko shan wasu miyagun kwayoyi, ko kuma yawan zubar da ciki, kuma hakan yana iya faruwa idan aka samu mace mai yawan bin maza, hakan zai iya haifar da kamuwa da manyan cututtukan da zasu iya lalata mahaifar.
ganyen gwaiba
ganyen lemun tsami
garin rumzali
kananfari rabin gwangwani
ruwa lita biyar(5lt)
sai a hadasu wuri daya a dafasu, sai a tace idan antace sai a rinka shan karamin kofi sau biyu a rana safe da yamma, zai wanke mahaifa da tsaftaceta da kuma kashe duk wata kwayar cuta da zata iya shiga cikin mahaifa ta kawo illa ga lafiyarki.
Allah Ya sa a dace
Comments
Post a Comment