Main menu

Pages

MAHANGAR ADDINI DA KIMIYYA GAME DA BANGON DUNIYA

 


Gaskiyar magana game da bangon Duniya a addinance da kimiyya

A duk lokacin da aka ambato kalmar bangon duniya, abu na farko da ke faɗo wa mutane da dama a rai shi ne ƙasar China, wasu kuma sai su fara tunanin wani dogon bango da ya raba duniyar da muke ciki da wata duniyar ta daban.


A addinin Musulunci an yi batun wasu halittu da ake kira Yajuju wa Majuj da za su shigo daga bayan wata katanga, wadda mutane da yawa suka ɗauka cewa katangar ce bangon duniya.


Shin yaya abin yake? Haka kuma shin akwai bangon duniya a zahiri da gaske?

BBC ta yi duba kan wannan lamari a mahangar addini da kimiyya.


Mahangar kimiyya

A wata hira da BBC ta taba yi a shekarar 2017 da Farfesa Yusuf Adamu, malami a tsangayar fannin nazarin ƙasa a Jami'ar Bayero da ke Kano, ya yi bayani kan batun bangon duniya.


A cewarsa, "duniya tana da bango kuma ba ta da bango", domin idan Bahaushe ya ce bangon duniya, yana tunanin cewa akwai wani waje, wanda idan ka je wurin, shi ne ƙarshen duniya.


Farfesan ya ce shi Bahaushe tun asali idan ya tashi daga wani gari zuwa wani gari akwai ganuwa ko kuma bango da ya zagaye garin, shi ya sa yake tunanin ita ma duniya akwai inda za a je a ga irin wannan ganuwar a ƙuryarta.


Duniya a zagaye take ba bango

Farfesan ya ce a zahiri, babu wani bango da za a ce ya kewaye duniya baki ɗaya.


"Akwai wurin da manazarta da yawa suke ɗauka a matsayin bangon duniya, abin da manazarta da matafiya suka gano shi ne tana da ƙarshe a sama da kuma ƙasa.


''Akwai inda ake ce wa North Pole da kuma South Pole, wato bangon duniya na arewa da kuma bangon duniya na kudu."


A cewarsa, waɗannan wurare duk ba a wata ƙasa suke ba, sai dai akwai ƙasashe da dama da sukan je su kafa tutocinsu a wurin.


"Akwai mutane ƙalilan da ke zaune a waɗannan wurare waɗanda ke gudanar da bincike, haka masana kimiyya su ma suna zama ne na taƙaitaccen lokaci su bar wurin sakamakon wurin ko yaushe a cikin ƙanƙara yake.


A cewar Farfesan, waɗannan wurare wata shida ake yi ana dare haka kuma wata shida ake yi ana rana, kuma ko da yaushe wurin a ƙanƙare yake, akwai kuma dabbobin da Allah ya halitta da ke rayuwa a wuraren.


Shin China ce Bangon Duniya?


A cewar Farfesa Yusuf Adamu mutane na tunanin cewa bangon duniya a China yake saboda wata ganuwa da ake da ita a ƙasar mai tsawon gaske.


"Ganuwar China na da girma da faɗi, ta fi kilomita dubu, tana da tsawo sosai, saboda haka idan wani ya je can sai ya ɗauka wannan ganuwar ita ce bangon duniya."


Hakan na faruwa ne saboda mutane sun kuma ɗauka China ce ƙasa ta ƙarshe a duniya, amma abin ba haka yake ba don Japan na gaba da China sannan daga nan sai ruwa sai kuma a zagaya a shiga Amurka, tun da duniyar kamar ƙwallo take.


Binciken masana ya nuna cewa ganuwar ta China na da tsawon kimanin sama da kilomita 21,000 inda aka ɗauki sama da shekara 2,000 ana gina ta.


Sama da masu yawon buɗe ido miliyan 10 ne ke kai ziyara zuwa ganuwar ta China a duk shekara.


Mahangar addini

Domin ƙara tabbatar da ko da gaske akwai bangon duniya a zahiri a mahangar addini, BBC ta tuntuɓi Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah, wani malamin a Najeriya, inda ya ce a addinin Musulunci babu wani wuri da aka ce shi ne bangon duniya, domin babu inda aka ce aljanu ko mutane sun gina wani bangon duniya.


Ya ce ko a Al-Ƙur'ani da aka ce Sarki Zurkallaini ya gina katanga saboda Yajuju wa Majuju ba yana nufin cewa wannan ginin a ƙarshen duniya yake ba.


A cewar malamin, sarkin ya yi ginin ne saboda yadda Yajuju wa Majujun ke tsallakawa domin yi wa wasu mutane ɓarna.

Comments