Yadda Ake Cabbage Rolls
Nama
kabeji
Attarugu
Koren tattasai
Albasa
Magi
Karas
Kori
Citta
Tafarnuwa
Man gyada
Hadi:
A wanke nama sannan a markada shi a na’urar nika nama a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta da gishiri kadan sannan a samu kabeji a bare shi manya-manya a tafasa da gishiri kadan na tsawon minti biyar. Sannan a tsame a ajiye a gefe.
A dora tukunya a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da nikakken naman a zuba magi da kori da garin citta da tafarnuwa da jajjagen attarugu da yankakken koren tattasai a yi ta gaurayawa har sai naman ya nuna ya soyu sannan a kwashe.
A sami kabejin da aka tafasa sannan a shimfida shi kamar tabarma sai a debo hadin nama a zuba a ciki sannan a yi masa nadin tabarma a tottoshe gefe-gefen.
Sai a dora tukunya a kan wuta a zuba man gyada kadan ba mai yawa ba, sannan a zuba wannan ninkin kabejin a cikin man a soya sama-sama sannan a kwashe,
Za a iya cin wannan hadin kabejin da shayi mai zafi da safe a matsayin abin karyawa.
Comments
Post a Comment