Muhimman shawarwarin ga Mai ciki da abincin da za tana ci
1- Game da Abinci :
Idan mace ta samu ciki yaron da yake cikinta yana zukan jininta sabida shine abincinsa wannan dalilin yasa mata masu ciki suna yawan samun karancin jini .
Ya kamata mace mai juna biyu ta dinga cin abinci iri iri musamman abinci mai gina jiki kamar su :
- Wake
- kifi
- Nama
- kwai da sauransu
Dakuma ganye da kayan itatuwa kamar su :
- Salat
- kabeji
- Alayyahu
- zogole
- Lemu
- kankana
- Apple dasauransu .
Cin abinci lafiyayye yana karawa mata jini, lafiya, yana karawa yaron da yake cikin ta lafiya da kaifin basira.
2- Game da irin Zaman Mai Ciki :
- Mace mai juna biyu bai kamata ta dinga aikin wahala sosai ba, ya kamata tadinga hutu ko wacce rana .
- Idan Mace mai ciki bata da lafiya dole taje asibiti domin gudun kada tayi amfani da maganin da zai zama mata matsala ,ko zai iya kawo matsala ga yaron cikinta .
- Tsaftar muhalli da tsaftar jiki yana da amfani sosai ga mace mai juna domin kare kanta da yaron cikinta daga kamuwa da cututtuka .
- Macen da take yawan amai yakamata tayi amfani da busheshshen abinchi wanda hakan zai rage yawan amai ko kuma ya tsayar da aman gabaki daya .
3- Game da amfani da maganin Karin jini:
Mafi yawan Mata idan anbasu maganin karin jini mai makon suyi amfani dashi kullum, amma basa amfani da shi, da sunan basa son warin maganin , wanda wannan baya daya daga cikin dalilin da zaisa a hana mutum shan wannan maganin .
Asani dama can magani ba dan dadi ake shanta ba, illa dan neman lafiya da neman kariya daga lafiya .
4- Game da alluran Tetanus :
wannan wata allurace da akeyiwa mata lokocin awun ciki , amma mafi yawa mata basa son wannan allurar sabida rashin sanin amfaninta .
Gaskia wannan allurar tanada amfani sosai wanda yana daga cikin amfaninta shine kare yaro daga kamuwa da wannan cutan nan mai hatsarin gaske wato ( tetanus ) .
Sai Kuma Zuwa awo, Mace mai ciki tayi kokari ta dinga Zuwa yin awo asibiti don sanin lafiyar ta da abinda ke cikinta.
Comments
Post a Comment