Albishir ga Masu lazimtar karatun Qur'ani
1. Kyakkyawan Hadisi Daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: 'Idan mutum ya mutu danginsa suka shagaltu da jana'izar sa,wani kyakkyawan mutum zai tsaya a kansa a Lokacin da ake rufe jikin mamaci, wannan mutumin yakan shiga tsakanin mayafin da kirjin mamacin.
Lokacin da aka gama binne sa, mutane suka dawo gida, mala'iku 2, Munkar da Nakeer (Mala'iku biyu na musamman masu tambayar kabari), zasu zo cikin kabarin sa suna kokarin raba wannan kyakkyawan mutumin da mutumin da ya mutu, don su sami damar yi wa mamacin tambayoyi a game da imaninsa.
Ammaa kyakkyawan mutumin nan zai ce, 'Abokina ne shi. Ba zan barshi shi kaɗai ba. Idan an nada ku don yin tambayoyi, kuyi aikinku. Ba zan iya barin shi ba sai na shigar da shi Aljannah '.
Bayan haka sai ya juya ga abokinsa (mamacin nan) ya ce, 'Ni ne Alkur'ani, wanda ka saba karantawa, wani lokacin da babbar murya wani lokaci kuma da karamar murya. Karka damu. Bayan Munkar da Naker sun game maka tambayoyi, ba za ka sami baƙin ciki ba. '
Lokacin da Munkar da Nakir suka ƙare tambayoyin su ga wannan mamacin, sai kyakkyawan mutumin nan ya shirya masa daga Al-Mala'ul A'laa, shimfiɗar siliki cike da miski.
2. Annabi (SAW) ya ce: 'A ranar sakamako, a gaban Allah babu wani Mai Ceto da zai sami matsayi sama da Alkur'ani, ba Annabi ko Mala'ika.'
3. Don Allah a tura wannan 'Hadisin' zuwa ga Yan uwa muslmai .... saboda Annabi (SAW) ya ce: 'Ka bada ilimi daga wurina ko da aya ɗaya ce'. Allah Ya bamu iko.Ameen
4. Muna addu'ar wannan sakon da muka kawo zai isa zuwa ga musulmai akalla miliyan biyar a duk faɗin duniya cikin kwanaki bakwai (7) masu zuwa, Insha-Allah. Da fatan za a tura wannan sakon a YAU ga abokai da dangi dan samun lada mai yawa daga Allah (SWT).
* Idan ka dauki Al-Qur'ani, Shaidan yakan kamu da ciwon kai.
* Idan Ka buɗe shi, sai ya fadi.
* Idan Ka karanta shi, sai ya suma.
* In kukayi kokarin tura wannan sako na Alkairi, zaiyi kokarin sanyaya muku gwiwa.
Comments
Post a Comment