Main menu

Pages

AMFANIN DABINO GUDA BIYAR(5) GA LAFIYAR DAN ADAM.




Amfanin Dabino biyar (5) ga Lafiyar Dan Adam.

Binciken masana da kwararrun kiwon lafiya ya tabbatar da cewa, kusan dukkanin dangin abinci ko na sha mai zaki da aka sarrafa na da matukar illa ga lafiya muddin aka yawaita ta'ammali da su, sai dai hakan bata kasance ga dabino ba. 



Babu shakka dan dabino na da tabarrakin sunadarai masu tarin yawa da ke gagarumin tasiri wajen bunkasa lafiya da yi wa jikin dan Adam garkuwa ta kamuwa daga wasu miyagun cututtuka. 

 


Dabino ya kushi sunadari kamar su;

Anthocyanidins,  carotenoids, acetylcholine, magnesium, calcium, potassium da makamantansu. Sanadiyar wannan sunadarai, ga wasu cututtuka da dabino ya ke kawar wa daga jikin dan Adam: 



1. Maganin gudawa; Dabino na maganin cutar gudawa da dukanin wasu cututtuka masu nabasa da ciwo ko lalacewar ciki da ake kamuwa da su.


 2. Cutar Daji(Cancer); Haka kuma dabino na maganin cutar nan ta ’Cancer’ mai kashe kwayoyin garkuwa. 


3. Dabino na kara lafiya; Dabino na kara lafiya inda yake karawa mutum kiba saboda wasu sinadarai da yake kunshe da su. Haka kuma yana tsaftace jinin mutum daga kamuwa da cutar ciwon sikari ko kuma cutar hawan jini. 


4. Dabino na kara karfi da kuzari; A dalilin irin sunadaran da ke ciki na Calcium, Sulphur, Iron da sauran su, Dabino na kara karfin kashi da kuma kwanjin mutum ya karu. Hakan ya sanya ake son fara cin dabino ga mai buda baki na sha ruwa bayan azumi domin kuwa yana kara karfi. Haka kuma ya sanya ake ba yaro da zarar an haife sa. 


5. Kara lafiyar kwakwalwa da kaifin basira; Dabino ya kunshi sunadaran Vitamin B da kuma Choline, masu taka rawar gani wajen bunkasa lafiyar kwakwalwa da kaifin basira. Haka kuma wannan sunadarai suna taimako wajen yin riga-kafin kamuwa da cutar mantau a yayin tsufa. 

Comments