Main menu

Pages

BABBAN ALBISHIR GA MASU YIN MINING PI NETWORK (π)

 



Babban Albishir ga Masu yin PI Network (π) Mining

Yayin da matasa da dama su ka bazama su na shiga harkar Pi (π), inda su ke kyautata zaton harka ce ta samun dukiya mai tarin yawa a saukake ta wayoyinsu ba tare da yin wani aiki karfi ko kuma zuwa wani wuri ba, Jaridar Labarun Hausa ta samu nasarar tattaunawa da shugaban ‘yan Pi na Tudun Wadan Zaria mai suna Abubakar Aminu Maude, wanda ya feda mana daga biri har wutsiyarsa dangane da harkar.



Da farko ya fara bayyana sunansa tare da yadda ya tsinci kansa a cikin wannan harka ta tara kudi a saukake kuma daga kwance. Ya ce ya dade yana jin labarin Pi, amma bai dauke shi da muhimmanci ba, yanzu kuwa da ya bincika kuma ya samu karin bayani dangane da harkar, ya yarda tabbas gaskiya ce.



A cewarsa, yanzu haka ya kai shekara daya da fara harkar kuma ya tara Pi fiye da dubu daya da dari biyarwadanda yake da ran nan ba da jimawa ba zai mori tagomashinsu. Abubakar ya ce da wayar salularsa ya samu manhajar wacce ba tare da ya sanya ko sisi ba ya fara tara abin duniya.



Ta hanyarsa akwai mutane da dama da su ka fara, kuma yanzu haka su kansu sun fara ganin irin yawan dukiyar da su ka tara a harkar. Yayin da wakilin Labarun Hausa ya tambayeshi ko akwai kasashen da su ka fara amfani da Pi, sai ya kada baki yace:



“Eh tabbas, akwai kasashen da su ka fara amfani da Pi wurin siyayyar abubuwa da dama. Kamar China da Indonesia, duk sun fara harkar. Yanzu haka ana sa ran nan ba da jimawa ba kowa zai yarda da Pi, kuma ya samu karbuwa a duniya.”


Bayan tambayarsa kimar ko wanne Pi daya a kudin Najeriya, ya bayyana cewa:

“Eh to, a yanzu dai babu inda aka tsayar da kimarsa. Sai dai ba Naira ba, ko dala, Pi ya fi su daraja. Don a kiyasin da ake yi yanzu haka, ko wanne Pi daya yana daidai da $314,159, wanda yayi daidai da N180,000,000 da ‘yan kai.”


Kuma a cewarsa, yanzu haka yana da Pi fiye da guda duba daya da dari biyar, wanda da Labarun Hausa ta yi kiyasi, idan ya sauya Pi dinsa a kudin Najeriya, zai tashi da kimanin N270,000,000,000.

To Allah Ya bada sa'a yYa tabbatar da Alkhairi Yasa kuna da rabon samun wadannan iyayen kudi, Ameen.


Comments