Main menu

Pages

GYARAN JIKIN MACE NA MUSAMMAN GA 'YAN KWALISA

 



Yadda ake gyaran jikin Mace na musamman.


Gyaran jiki musamman ga mace na da muhimmanci sosai. 

Domin mata da dama wadanda suke da kananan shekaru idan jikinsu ba ya samun sinadaran da suka kamata akwai matsala. 

Sai a ga fatar jiki tana yankwanewa. 

Yankwanewar fatar na sanya mace tsufa da wuri.

 Don haka, dole ne a rika kula da fatar jiki da gashi da sauran gabobi.


Gashi; a samu ayaba da kwai a cire kwaiduwar sannan a kwaba tare da ayaba sai a tsaga gashi a shafa a fatar kai hade da gashin kai sosai. A bari na tsawon minti goma zuwa ashirin sannan a wanke da man wanke gashi. Yin haka na sanya karfin gashi kuma yana hana shi zubewa sannan yana sanya shi sheki.



Farce; a samu zuma a rika shafawa a farce na tsawon minti biyar akalla sau daya a mako domin sanya farce laushi da sheki sannan za a iya shafa zumar a fuskar domin magance kurajen fuska.



Dilke; a samu dilke a rika shafawa a jiki kamar sau daya a mako, yin haka zai sanya fata santsi da sheki.



Tsayin gashi; a samu man kwakwa a rika yin kitso da shi ko a rika shafawa a fatar gashi duk lokacin da man ya shanye a kai. Yin hakan na sanya laushi da kuma tsawon gashi.



Kurajen fuska; a samu lemun tsami a yanka shi gida biyu sai a diga zuma kamar digo daya zuwa biyu. 



Sannan a shafa a kan fuskar na tsawon minti biyar. Sannan a wanke. Za a iya yin wannan da dare kafin a kwanta barci a kullum.



Fata; yawan shan ruwa na wanke maikon jiki sannan yana sanya fata lafiya. A kasance ana samun isashen barci a kullum domin samun fuska mai sheki.



Domin kodewar fata; a samu lemun zaki a rika shafawa a inda matsalar take kamar sau biyu a kullum har sai wajen ya kode.

Comments