NA SO MU YI SULHU TUN FARKO DOMIN KULA DA LAFIYAR FATIMA DA SAMAR MATA MAFITA, AMMA ABIN YACHI TURA DOMIN IYAYEN TA BASU BADA HADIN KAI BA...
Mamar Aliyu ta nemi Dangin Fatima su yafewa Aliyu,
Wata ɗaya da samun rahoton Yanke qafar Ɗaliba Fatima Alokacin Murnar Kammala jarabawar NECO ga ɗaliban makarantar Kalipha International Secondary School A jahar Sokoto, an lashe wata ɗaya cif ana kai Ruwa rana tsakanin Dangin Fatima da Dangin Aliyu wanda ya bige Fatima har Saida aka yanke ƙafarta..
Rahoton da muka samu daga Muryar Mamar Fatima Hajiya Hadiza, ta bayyana cewa babu Maganar yafiya. Koda Sama da qasa zasu haɗe baza su yafe ba sai an biya su Diyyar ƙafar Fatima. "Kuɗi Sunci ubansu"
Afirar da Mukayi da Mai baiwa Gomna Tambuwal shawara akan Hakkin Bil'adama Hajiya Ubaida Bello, ta shaida mana cewa a chikin zaman Sulhu da muka yi da Iyayen Fatima, Iyayen Aliyu da Jami'ai na Human Rights, mun tashi babu daɗin rai. domin Mahaifin Fatima ya gaya muna maganganu marasa dadi a idon mu. ya kuma tabbatar muna da chewa shi ba zai sulhunta da kowa ba sai dai a biya shi diyyar kafar ƴar shi da kuma diyyar ɓachin ran ta na har iyakar rayuwar ta.
A lokachin da Mukayi zama da Mamar Yaron tare da Ma'aikatan gidan Jaridu Jiya, Mahaifiyar chikin Muryar tausayi ta shaida mana cewa sunbi duk hanyar da za'abi wurin ganin an samu sulhu tsakanin su da Dangin Fatima tun farkon lokacin da abun yafaru zuwa yanxu, amma dangin Fatima basu aminta ayi Sulhun ba.
Mun bada duk abinda ake buqata ga lafiyar Fatima ba tare da kasawa Koh Gajiyawa ba amma iyayen basu haqura ba. Mun shaida musu mun ɗauki nauyin komai na Jinyar Fatima har zuwa samun Sauqi da Yimata qafar roba amma basu haqura ba. A duk Lokachin da naje asibiti domin duba Fatima hantara ta akeyi Na rasa bacchi narasa abinchi saboda yanayin Fatima inji Mamar Aliyu.
Mamar ta qara da cewa tafi tausayin yanayin Fatima da'aka yankewa qafa take fama da jinya asibiti fiye da Ɗanta Aliyu dake zaman gidan kaso tsawon wata ɗaya Ahalin yanxu...
A daidai Lokachin da wasu ke tausaya wa Fatima, wasu Mutanen ma suna tausayawa Aliyu zamanshi qaramin yaro a kurkuku chikin 6arayi da Kidnappers da Mashaya da Mahaukata da Mutane Masu hatsarin gaske. Har wasu ke gudun kar zaman sa gidan kaso yazama Silar sauyawar rayuwar sa zuwa wani Mutum na daban achikin Al'umma.
Mamar Aliyu ta rufe Magana Chikin kuka da zubda hawaye tana cewa wannan qaddara che daga Allah muna roqon ayi haquri a yafe mana!
Comments
Post a Comment