Main menu

Pages

HANYOYIN RAGE TEBA DA MUGUWAR KIBA TA FANNIN CIMA

 



Hanyoyin Rage Teba da Muguwar kiba ta hanyar Cima

Assalamu alaikum Warahmatullah

A yau zamuyi cikakken bayanin yadda za a rage Teba da Kuma kibar da tayi yawa sosai ta hanyar cin abincin da ya dace da lokacin da ya dace.


1. Ka tabbatar ka karya kumallo a kowacce rana, domin ƙin karin kumallo ba zai taimaka maka wajen rage ƙiba ba, sai dai ma ya hana ka samun kuzari a tsawon ranar da ba ka yi karin kumallon ba.


2. Ka ci abinci na yau da kullum. Domin hakan yana taimakawa wajen ƙone sinadarin (calories) a cikin sauri a lokutan da rana ta take.


3. Ka ci ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki a mafi yawan lokaci, domin ‘ya’yan itace da ganyayyaki suna da ƙarancin sinadarin ƙiba wato (fat).


4. Ka ƙara yawan motsa jiki ko ayyukan da kake yi na yau da kullum.


5. Ka sha ruwa mai yawa, kuma kada ka bar kishirwa a tare da Kai.


6. Ka ci abincin dake ƙunshe da (fiber) mai yawa, hakan zai taimaka maka jin ƙoshin lafiya, da rage maka teba da rage nauyi. Ana samun fiber a cikin abinci da tsirrai, irin su ‘ya’yan itace da ganyayyaki, hatsi, da shinkafa da taliya, da wake.


7. Ka guji cika cikinka da abinci, a maimakon haka, sai ka rinƙa haƙura da abincin kafin ka ji ka ƙoshi. Domin ciki na ɗaukar kimanin mintuna 20 kafin ya gayawa ƙwaƙwalwa ya ƙoshi.


8. Kada ka haramta wa kanka abincin da kake so, a maimakon haka, kawai sai ka rage yawan cin sa.


9. Ka musanya cin kayan kwalam da maƙulashe ya zuwa cin ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki.


10. Ka guji sha ko cin abin dake da sinadarin giya a ciki.


11. Ka tsara wa kanka lokacin cin abinci.


12. Ka hakura da lemukan kwalba da roba.


13. Ka hakura da cika ciki taf kafin ka kwanta bacci. 


14. Kasha Lipton da lemon tsami kafin ka kwanta in baka da ulcer hakan na taimakawa wajen kone kitsen tumbi


15. Rage cin abinci mai sugar sosai hakan na taimakawa wajen rage kiba


16. A samu isasshen bacci saboda sabon bincike ya nuna cewa rashin bacci sosai yakan taimaka wajen kara kiba (nasan wannan zai bada mamaki ga masu karatu)


17. A kwanta a mike sosai a kasa sai a danne kafa ana dagowa ana komawa kullum ana yi ana karawa yana maida tumbi sosai wannan. 


Za mu tsaya a nan sai an karo bincike kuma Allah Ya sa a amafana.

Comments