Yanda Zaki hada hadadden Tsiren Tukunyar a gida yayi dadi.
Yanda Ake Hada Tsiren tukunya, ga abubuwan da Zaki tanada.
Abubuwan hadawa
- Jan nama kilo
- Albasa
- Maggi
- Yajin barkono
- Kuli kuli (gari)
- Kayan kamshi
- Man gyada
- Koren tattasai
Yanda ake hadawa
Da farko zaki wanke namanki ki masa yanka mai fadi-fadi ki ajiye a gefe.
Sai ki hada yajin da man gyada da garin kulikulinki ki sa maggi da kayan kamshi sai ki kwaba.
Sai ki dinga shafawa a jikin naman gaba da baya.
Idan kin gama sai ki kawo tukunya ko kasko (frying pan) mara kamu sai ki jera ki dora a wuta ki rufe ki barshi. Kar ki sa wutar tayi yawa.
Sai ki ringa juyawa, idan yayi sai ki sauke ki yanka dai dai misali kisa a pilet ki yanka albasa da koren tattasanki.
Sai a sawa maigida da yara aci Lafiya.
Comments
Post a Comment