Main menu

Pages

ZAMANTAKEWAR AURE ABUBUWAN DA KESA A ZAUNA DA MACE LAFIYA




Zamantakewar Aure - Abubuwan dake taimakawa a zauna da Mace Lafiya.

Yace ya kai da Na, hakika ba zaka taba samun jin dadin zamantakewar aure a cikin gidanka ba har sai ka kiyaye dabiu (10) da zaka mu'amalanci matarka dasu don haka ka kiyaye su


Na Daya da na Biyu : 

Hakika su mata suna son tausasawa da ja ajiki kuma suna son a dinga cewa ana sonsu ana kaunarsu. Don haka kada ka dinga yi musu rowar fadar haka, idan kuwa ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakaninka da ita na samun Karancin soyayya da kauna.



Na Uku: Ka sani cewa su mata ba sa son mutum mai tsanani mai mugun takurawa, idan ka fahimce su, suna yiwa mutum rarrauna hidima. Don haka kowacce sifa ka ajiye ta a gurin data dace domin hakan shi zai fi jawo kauna da nutsuwa a tsakaninku



Na Hudu: Hakika su ma mata suna son irin abinda namiji ya ke so daga gurin mace, kamar daddadan kanshi, magana mai dadi, kyak-kyawar Shiga, tashin kanshi da dai sauransu. To don haka ka sifantu da dukkan wadannan halaye a dukkan yanayinka



Na Biyar: Ka sani cewa Gida wata masarauta ce ta mace wadda take jin cikakken iko a cikinta kuma take jin cewa itace shugaba a cikinsa. To ina Jan kunnenka da Kada ka kuskura ka rusa wannan masarauta, kana mai Nuna mata cewa ita ba kowa bace ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abinda ka so, idan kayi haka to ka tumbuke ta daga kan sarautarta, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a Duniya fiye da Wanda ya sauke shi daga kan mulkinsa.



Na Shida: Dukkan mace tana son ta yiwa mijinta hidima amma kuma bata son ta rabu da 'Yan uwanta, to kada kayi kokarin raba ta da danginta ta hanyar bats zabin ko kai ko danginta, domin idan ta Zabe ka akan danginta to babu shakka zaka dawwama cikin bakin ciki da Bacin rai da za ka dinga samu daga gare su.



Na Bakwai: Hakika ita mace an halicce ta ne daga kashin hakarkarin namiji karkatacce, wannan kuma ba aibu bane a gareta shi ne ma kuma sirrin kyawunta da kuma Jan hankali..

Comments