Main menu

Pages

ALAMOMIN DA KE TABBATAR DA CEWA ASUU TA KUSA JANYE YAJIN AIKI

 



Wadannan alamun sune suke tabbatar da Asuu ta kusa janye yajin aiki

Wasu rassan kungiyar malaman jami`o`i a Najeriya, sun fara duba yiwuwar janye yajin aikin da suke ko kuma ci gaba.


Tuni rassan kungiyar suka gudanar da taruka domin yanke shawara a kan daukar matakin da ya dace.




 A ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba ne ake sa ran shugabannin rassan kungiyar za su kai ra`ayoyin rassan wajen taron da shugabannin uwar kungiyar za ta yi don daukar mataki na gaba.




Rassan kungiyar malaman jami`o`in sun yanke shawarar gudanar da tarukansu ne bayan shiga tsakanin da kakakin majalisar wakilan Najeriyar ya yi, wanda bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shaida wa`yan kungiyar cewa akwai haske sosai.




Tuni dai wasu rassan kungiyar malaman jami`o`in suka fara tattaunawa a matakin rassa da kuma shiyyoyi alamar da ke nuna cewa akwai bayanin da suka samu, wanda kuma suke yanke shawara a kan sa.




Farfesa Muhammad Nuraddeen shi ne shugaban reshen jami`ar Usman Danfodio na kungiyar malaman jami’oin, ya shaida wa BBC cewa duk maslaha alheri ce ga bangarorin da wani abu ya shafa.




 Farfesan ya ce, a cikin watannin da suka shafe suna wannan yajin aiki ba su taba samun wani bayani daga gwamnati da ya nuna da gaske ta ke kamar a yanzu da kakakin majalisar wakilai ya shiga ba.




Ya ce,” Ina ganin cewa wannan maslaha za ta zamo alkhairi ga su kansu dalibai da iyayensu da mu kanmu malamai da kuma al’umma.”




Kungiyar malaman ta ASUU, ta shafe kusan watanni takwas ta na yajin aiki domin neman a inganta wa ‘ya’yanta albashi da wasu kudaden alawus, tare da samar da isasshen kudi don inganta koyarwa a jami`o`in.




Wannan ci gaba da aka samu da ke nuna alamar an kusa kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’oin ke yi zai iya zama babban albishir ga dalibai da ma iyayensu.

Comments