Illar Shan maganin zak'i ga mai ciki, da matsalar da ka iya biyo bayan Shan magungunan.
Yar uwa ki jiƙa abu kaza da kaza kisha domin ki fitar da zaƙin dake mararki kafin naƙudar haihuwa, ko kuwa wane karɓi wannan maganin ka kaiwa wance kace ta jiƙa ta rika sha maganin zaƙi ne.
Wadannan sune irin maganganun da zakaji suna zagawa musamman tsakanin Mata in sun hadu da mai juna biyu. Toh amma fa
A likitance ba musan wani abu wai shi zaƙi a marar Mace ba ballantana fitarsa ajikin Mace gabatowar haihuwa.
Hakika duk da irin wannan al'ada ta jima amma duk da haka mun shigo wani zamani yanzu da gurbatattun labarai da bayanai marasa sahihanci na ilimi suka yawaita tsakanin al'umma.
Komi mutane sukaji ba duk ke tsayawa suyi nazari da binkice ba akan;
▪︎Shin kaza din nan da akace yama dace kuwa?,
▪︎Dadin abun aka fada amma menene illar daka iya biyo baya?
▪︎Shin hakan ma batun yake a ilmance ko kuwa?
Wannan tasa da zarar haihuwa ta gabato Mace kowa sai kaga shawara yake ba Mai ciki akan komi ma, musamman atsakaninsu Mata..., Eh munsan kuna yine bisa kyakkyawar manufa da son kuga ta haihu lafiya.... ammafa ba duk yan adam bane zubin halittarsu tare da komi yai daidai dana juna ba.
Ba mamaki wata kukaji tayi irin haka ta kwana lafiya amma mu tuna fa idan wani yai abu ya kwana lafiya to fa wani in yayi wahala zai sha.
Babu wani abu da sunan zaƙi jikin mai juna biyu, in akace zaƙi ajika tofa mu ko yaushe abunda muka sani, ana batu ne na ciwon suga ajikin mutum. wato sinadarin glucose acikin jini. Shi ko ciwon suga yayin goyon ciki "gestational diabetes" sunansa kuma muddin aka ganosa ba'a wata-wata ake dora Mace kan abinci ko magunguna wasu lokutan allurar insulin domin bata kariya daga hatsarin suga wanda cikin hatsarin akwai mutuwar yaro aciki, mutuwa wajen haihuwa, zubewar ciki, ko sanya jariri yai girma fiye da kima aciki ta yadda bazai iya haifuwa ta farji ba saide ai aiki acirosa ko kuwa sai anqara fadin farjin Mace kafin kansa ya wuce.
Wasu kan dauka kowanne katoton jariri abun sone, Amma wani girman bana ka'ida bane galibi alamace ta larurar suga yayin goyon ciki a macen, musamman a macen da bata rika zuwa awo ba, kurum an auna arziki ne. Duk jaririn da nauyinsa ya wuce 3.5kilogram mahaifiyarsa abin zargi ce.
Ita kuwa wannan sugar bazata ta6a fita ta farji ba kota hanyar fitar da wani ruwa
Don haka abunda muka sani na ruwa ajikin Mace dake fara leaking gabatowar haihuwa shine ruwan da ake kira AMNIOTIC FLUIDS wanda kuma wannan ruwane da jariri kan fara taruwa tun daga sanda ciki yai sati 4 inda ake fara iya ganinsa a scanning tun daga sati 8 na juna biyu.
Wannan ruwan amniotic cikinsa jariri ke rayuwa, yana kuma samuwa ne daga abunda Macen kesha na abinci da kuma fitsarin jaririn. Eh jariri na fitsari tun aciki wanda shine wannan amniotic din kuma akarshe shine zai shanye abinsa yayin kishirwa da kansa sannan ya qara fitsarar dashi, haka zaita recycling duk bayan awa 3, saboda mabiyiya (placenta) dinsa na tace masa shi.
A kullum sai jariri yai fitsari kwatankwacin Moɗa biyu wato 500milliliter.
Wannan ruwan har ila yau da taimakonsa; Jariri ke motsi da juyi aciki, shike taimakawa huhun jariri samuwa, shike sa ciki girma, shike samarwa da jariri kyakkyawan yanayi wato tempreture, saukin naƙuda tare da samuwar cikakkiyar halittar dan adam ajikinsa ya zamto ba'a haifesa da tawaya ba irin; karamin kokon kai, guntulallen hannu, yamutsatsiyar fata, kayan ciki awaje, dade sauran ababen gudu masu illah.
Toh menene ma yasa ake kiran ruwan da zaƙi?
Watakila sakamakon kalar ruwan amniotic din ne da takan canza ya zamo yayi kalar kasa-kasa kamar dafaffen ruwan sikari me kauri shiyasa mutane ke kiransa da ruwan zaƙi tunda yai kalar dafaffiyar sugar amma ba zaƙin ne dashi ba suffarsa ce kurum kamar abun zaƙi a ido. Hasali ma inda mutum zai dandanasa zaiji kamar ďanďanon kori yake.
Ruwane da afarkon ciki kalarsa haskene dashi kamar ruwan sha, saide yayin da ciki ya tsufa yakan canza launi sannan yawansa ya fara raguwa ta yadda yake fara fita ayayin da ciki ya gama cika watannin isa haihuwa wato sati na 37, 38, 39, ko 40.
Wannan ruwan yana fara fita alamace ta bakin mahaifar Mace na shirin soma budewa (cervix dilatation) wato naƙuda wanda ke nuni da ta shirya cikinta zai fara murdawa (contraction) domin juye lodin dake cikin mahaifarta na tsawon watanni (jariri).
Abun tsoro shine ace wannan ruwan ya soma fita alhalin ciki bai gama cika watanninsa ba, ko kuwa ce ba haihuwar bace ta gaske, shine ma muke kiran irin wannan mugun yanayi da premature membrane rupture wanda hakan na nuna za'a haifo bakwaini ko kuwa wanda de bai gama cika watannin haihuwa ba. Infact yaron ma na iya mutuwa tun aciki sannan hakan zai barki da infection me tsanani da zai iya keta mahaifarki yai miki illa ko bayan haihuwa.
Don haka anan nake jan hankalin Matan mu game da wannan kuskuren na shaye-shayen abubuwa da sunan wannan ruwan ya fashe ya rika fita tun kafin lokaci haihuwa bisa tunanin cewa zaƙi ne kuma abune dakan iya jawo matsala wajen haihuwa. Toh gaskiya karatun ba haka yake ba.
In wannan abun ya fashe alhalin ba nakuda bace toh wannan kesa yaro ya makale wajen haihuwar saide aiwa Mace aiki, kota haihu a wuyace, ko ma ta haihu jini ya 6alle tazo ita ta mutu, ko yaron ya hadu da infection kwana 1 biyu ko sama da haka su jariri ya mutu.
Ya dace ai hankali asan cewa yanzu kullum kara wayewa al'umma take, ke da hankalinki tunda kike zuwa awo wato antenatal care baki ta6a jin ma'aikatan lafiya sunce miki ga wani magani da zaki sha ba saboda ki fitar da zaƙi gabannin haihuwa don gudun matsala toh ko wannan bai iya ku gane ba.
Inma al'adace aka gada yau ina al'adar zubar da colostrum wato ruwan nono na farko me ruwan rawaya-rawaya ko zallar madara me kauri bayan haihuwa....! Da iyayen mu matsesa ake azubar ace ai illah ne dashi ba'a baiwa jariri, inma Mace ta kasa matsoshi babbane zaisa baki ya zuƙe mata shi har sai sun tabbatar sun zubar dashi.
Amma bayan binkicen masana akan hakan sai gashi angano ai wannan ruwan nonon da ake zubarwa na farkon yafi duk wani abu da jariri zaici ko yasha inganci, yafi kowanne ruwan nono inganci tare da habbaka lafiyar jariri da basa kariya daga cuttuka. Yau bagashi sai tarihi ba, wasu ma basusan anrika hakan ba abaya.
Kusani wanna ruwan bazai ta zama har abada ba, shi akaran kansa da lokacin haihuwa yazo zai huje ya soma fita wanda hakan shi zaisa bakin mahaifa taushi ya bude yai santsi yadda jariri zai fita cikin aminci.
Wannan shine sakon, ku dena shan komi, inkuma anqi toh Allah raba bawa da wahala.
Comments
Post a Comment