Cikakken Bayani akan Batun Canza Fasalin Takardun Kuɗin Nijeriya
Jiya Gwamnan Babban Bankin Nigeria ya fitar da sanarwa cewa zai canza launi da fasalin kudin Nigeria domin kudin sunyi yawa kuma a sake tsaftace kudin da ga na 'yan damfara wadanda suke buga jabu, a cewarsa.
Wani bawan Allah ya ce; duk wannan rubutun harafin Larabci 'Ajami' shine ya tsole musu ido, anyi nasaran cirewa a ₦5, ₦10, ₦20, ₦50 da ₦100; shiyasa yanzu suke son su sake cirewa.
Takardun kudaden Naira da canjin zai shafa sun hada da takardan Naira ₦200, ₦500 da Nair ₦1,000 sune 'notes' da suka rage, masu rubutun 'Ajami' harafin Larabci na Musulunci a jikinsu, idan sun samu nasaran cire wannan a watan December yanzu sauran "نصر من الله" na jikin bajin sojojin Nigeria ya saura.
Kafin zuwan Turawa, yankin Hausawa, Musulmai, da 'script' na 'Larabci' suke amfani wajen rubuce-rubuce don isar da sako, wannan dalili ya sa aka rubuta ajami a jikin takaran kudin ₦aira.
Larabci harshe ne, eh! Kuma shi ne 'official language' na addinin Musulunci; amma ba shi ke nuna Musulunci ba, don akwai Larabawa da ba Musulmai ba.
Idan ba'a manta ba, watannin baya kadan wani Lauya makiyin Musulunci ya shigar da kara Kotu domin a cire harafin Larabci daga jikin takardun kudin Nigeria saboda kyamar da yake yiwa Musulunci.
Shi kuma Malam Adam Baba Yamani cewa yayi:
Haka gomnatin Buhari ta 1984 ta yaudari al'ummah ta chanza Naira cikin sati biyu, wanda hakan ya janyo hasarar dukiya ga wadanda ba su samu chanza kudaden da ke hannunsu ba, Naira ta rasa karbuwa da yawa a duniya kamar Dollar, kafin Buhari ya chanza Naira a 1984, Naira ta na yawo a ko ina cikin duniya, amma yana chanza ta, sai ta rasa karbuwa da kima.
An zo yanzu kuma a 2022 ya dawo ya sake chanza Naira domin ya kara nakasata, da ma kuma akwai aniyar karya darajar Naira zuwa 1000 ga Dollar America, yanzu za a tabbatar da wannan kudirin IMF akan 'yan Nigeria, duk wannan hauragiyar don a dafa masa ya gama mulki lafiya, shi bai damu da halin da Kasa da al'ummar Kasa za su shiga ba, shi dai ya yi mulki.
Dalilan da gomnati ta bayar na cewa kudaden da ke yawo sun yi yawa, da kuma akwai kudaden bogi da yawa ba gaskiya ba ne, in ma gaskiya ne, shin chanza kudaden ne maslaha ?
Zamu jira mu gani.
Allah Ya bamu mafita na alheri
Comments
Post a Comment