Main menu

Pages

GARGADI GA MASU GOGE KUNNE DA COTTON BUD DA WASU KEYI

 



Tattaunawa da ƙwararren Likita akan illar goge cikin kunne da cotton bud da wasu keyi.

Wani ƙwararren likitan kunne, hanci da makogwaro a jihar Enugu Chijioke Anekpo ya yi karin haske kan illar dake tattare da goge kunne da mutane ke yi wai don tsaftace su.




A hirar da ya yi da PREMIUM TIMES Anekpo ya yi kira ga mutane da su daina saka auduga a kunnuwan su wai don tsaftace kunnuwan su,saboda illolin dake tattare da yin hakan.




PT: Shin saka abin sauraren kiɗa wato ‘Ear piece’ ko ‘Headset’ na da kyau ko a’a?


Anekpo: Tabas Akwai illa amma haka din ya danganta da yawan karan sautin da mutum ke ji ne. Yawan haka na yi wa kunnuwar mutum illa.


Sannan kuma likita ya yi karin haske akan wasu abubuwa da ke kawo lahani ga kunnuwar mutane da kuma waɗanda basu kawo matsala.




” Babu matsala idan ruwan sabulu ya shiga wa mutum cikin kunne a lokacin da yake wanka.

ko da ruwa ya shiga kunnen mutum yana fita da kansa bayan wani lokaci.




PT: Akwai illa ne idan mutum na goge kunnen da abin goge kunne wato ‘cotton bud’ ?


Anekpo: Bai kamata ana goge kunne ba domin kunne bangaren jikin mutum ne dake iya tsaftace kansa sai dai mutane da dama basu san haka ba.




Ya ce mutum zai iya goge wajen kunnen sa amma ba ciki ba saboda illan dake tattare da yin haka.


Likitan ya ce kamata yayi daga haihuwa har zuwa ranar da mutum zai mutu kada ya goge cikin kunnen sa musamman da auduga. Akan samu matsala a wasu lokuttan inda audugan na iya makalewa a cikin kunnen mutum ya kawo masa matsala.





PT: Shin Akwai illla shan ruwan sanyi musamman ga makogwaro?


Anekpo: Babu ko daya. Amma ruwan sanyi na iya cutar da mutum idan har bai saba shan ruwan ba.


Shan ruwan sanyi ga wanda bai saba ba ka iya sa mutum ya kamu da tari ko mura.


PT: Shin Shan ruwan dumi na da illa ga lafiyar mutum?





Anekpo: Ba shi da illa amma a tabbatar cewa ruwan bashi da zafi sosai domin idan akwai zafi kuma aka sha zai kona baki.


PT: Shin Aske gashin hanci na da illa ne?


Anekpo: Akwai illa sosai idan ana yawan aske gashin hanci.


Gashin hanci na taimakawa wajen kare datti ko kura da mutum zai iya shaka.


Ya ce bai kamata a aske gashin dake cikin hanci ba amma za a iya rage tsawon gashin.





PT: Shin akwai wani illa idan mutum na yawan kwakule tasono daga hanci?


Anekpo: Akwai illa sosai domin yawan cire tasono daga hanci ne ke kawo habbo.


PT: Shin yawan amfani da takunkumin fuska na iya cutar da lafiyar mutum?


Anekpo: Akwai illa amma ga wadanda ke fama da cututtukan dake kama huhu da zuciya baya ga haka takunkumin fuska ba shi da illa ga lafiyar mutum.





PT: Shin hayaki daga ababen hawa ko daga itacen girki na cutar da lafiyar mutum?


Anekpo: Hayaki musamman daga ababen hawa na cutar da lafiyar mutum domin a cikin hayakin akwai sinadarin ‘carbon monoxide’ wanda ke cutar da zuciya da huhu.

Comments