Ingantaccen Turaren wuta na musamman, na Matan Aure kadai, Uwargida ko Amarya.
turaren wuta na daki wanda ke tafiya da kowanne zamani da kowacce mace amarya ko uwar gida matukar tanason miji ya zama me zumudin zama a dakinta tareda zumudin dawowa dakinta, kai wannan shine turare da matan aure kadai keyinsa,
suma akwai sharadi sai wanda sukeda tabbas akan miji ne kadai zai shiga dakinsu domin wannan turaren dakin ba'a sakashi a lokacin abari wani ya shiga dakin koda kuwa 'yar uwaki macece, shiyasa akeso kada kisaka sai da dare kafin miji ya dawo saiki saka shi kamar yanda zakiyi turaren wuta ki turara dakinki dashi,
Ingantaccen hadine Wanda Zakiyi mamakin yanda kamshinsa ke canjawa a daidai lokacinda kika saka shi, amma ki fara lura da kayan hadin wanda suke canja kamshinsa wanda bayaga itatuwan turaren wuta kamarsu
Sandal
Hawi
Gab-Gab
Durot
Ouhd
duka wadannan kowanne zaiyi sai kuma madarar turare shima kowanne za'asamu ya zama me kamshi sosai, Wanda kamshinsa bazai damu mijinkiba wadannan sune ake fara hadawa da farko,
Sai kuma asalin maganin wanda su kuma itatuwan ake garinsu ana hadawa dashi turaren wutan amma anaso ya zama yawansu daya kada garin maganin yafi turaren yawa,
Tsaiduwa
Furen rumfu
Furen tunfafiya
Kafi Malam
Ganyen Dan mannau
Shine turare dake Hana miji doguwar hira haka zalika ya hanashi Zama a turaka kamshinsa kadai ya isa yaha hankalinsa izuwa gareki.
Comments
Post a Comment