Main menu

Pages

HANYOYI TSARIN IYALI A LIKITANCE DA ILLOLIN DA SUKE HAIFARWA GA LAFIYA

 




Hanyoyin kayyade iyali / tsarin iyali da illolinsu ga rayuwar al'umma.


Kayyade iyali ko tsarin Iyali: na nufin tsara haihuwa, musamman matan da suke saurin daukar ciki, da kuma marasa lafiya. Rashin lafiyar da ake dauka wanda kan iya samun jariri, da kuma mutane da suke dauke da nauyi mai girma a kansu ba su da mai taimaka masu wajen warware matsalarsu. Wannan tsarin ya shafi mutum daya ne da iyalinsa a kankansa. 





Akwai hanyoyi ko dabaru da dama da ake bi wajen hana haihuwa ko kayyade iyali, daga ciki akwai:

• Kwayoyin magani na hana haihuwa

• Allurar hana haihuwa

• Zaren mahaifa

• Robar mata

• Robar maza (kororo roba)

• Kwayoyin magani masu hana haihuwa (Oral Contraceptives (PILLS)





wadannan kwayoyi ne da ake amfani da su don hana haihuwa. Asalin irin wadannan kwayoyi suna yin tasiri ne ga maniyyin mace su hana su aiki. Daga cikin Wadannan kwayoyi akwai wanda ake kira "ancullor" akwai "lyndiol" akwai kuma "liynovlor" da sauransu.





Allurar hana haihuwa (Projestin Injection)

Ita kuma wannan allura ce da akan yi don hana haihuwa. Daga cikin alluran da aka fi amfani da su don wannan aiki akwai kamar su "Depo-provera medroxy progestere Actate (DPMPA), da "Nokethindrone Enonthate (NET) da sauransu. Ita wannan allurar tana hana ciki ne ta wajen danne karfin kwayoyin maniyyin mace. Tana kuma kade jikin mahaifa ta yadda ko da ba ta yi tasiri ba kwan maniyyin ba zai sami inda zai makale a mahaifa ba, tana kuma tara majina mai kauri a hanyar da maniyyi kan wuce zuwa mahaifa, don kada ya samu wucewa.





Zaren mahaifa (Intra Uterine Devices (IUD)

Ita ma wata hanyar ce ta hana haihuwa wadda Richter da Graefenberg suka kago a shekarar 1909. Wani zare ne na roba wanda akan sanya a mahaifa a bar shi sai zuwa wani dogon lokaci. Ba za a cire ba sai sanda matar ke son ta sake haihuwa. Wannan zare yana hana maniyyi kuzari ya kuma kashe kwayoyin maniyyi na mace da kwaroron da sukan bi zuwa mahaifa.





Robar mata (Diaphragms and Cervical Caps)

Ita kuma wata roba ce mai tattausan baki. Wani likita ne a Kasar Jamus mai suna Ferick wilde ya kago shi a shekarar 1838. Ana sa wannan roba ne a cikin farji kafin saduwa ta yadda zai je ya toshe kofar mahaifa. Ana kuma shafa wani mai wa roban kafin a sa.





Wadannan kadan kenan daga cikin dabarun da akan yi amfani da su don hana haihuwa. Ba a ma yi maganan riga ba, wato kororon roba, wanda maza kan yi amfani da (condoms) da kumfa wanda mata kan sa, (foams). Akwai kuma hanyoyi da ake bi a dakatar da haihuwar gabadaya, wanda ake kira "Sterilization".  





Duk wadannan dabaru da muka ambata dabaru ne wadanda ilimin likitanci ya kago, wanda imma dai su zama na sha, ko kuma na sanyawa da wani abu, ko ta hanyar allura.


A post na gaba zamu kawo maku illolin kowane su Insha Allah.

Comments