Main menu

Pages

ILLOLIN DA KE FARUWA GA MA'AURATA IDAN SUNA RABA DAKI

 



Shin 'yan uwa ko kunsan yawan illar da raba daki da miji da wasu keyi ke haifarwa?


Toh Ku saurara Kuji abubuwan dake faruwa:-

1- Yana rage kusanci da shakuwa a tsakanin  ma'aurata.




2- Yana sa ma'aurata su rika jin wani iri wajen neman juna don raya sunnah Mace zata ki zuwa wajen mijinta tace ai idan yana da bukatarta ya nemeta, shi Kuma miji ya hakince a dakinsa yaki zuwa wajen matarsa yana jira sai ta biyoshi, karshe sai dai su rungumi Pillow su kwana suna jin haushin juna.




3- Yana sa fada yayi tsawo a tsakanin ma'aurata idan sun samu sabani, sai a dauki kwanaki basu shiryaba.




4- Yana sa miji ya samu daman yi wa matarsa iyaka da wasu abubuwanshi dake cikin dakinsa




5- Yana sa Mace ta rika jin dar-dar duk lokacin da ta shiga dakin mai gida da niyyar kwalema ko neman wani abu, musamman idan ya shigo ya taradda ita a ciki dakinsa tana dube-dube ko neme-nemen wani abu


.



Hikimar kwana daki daya da Miji;

1- Yana sa shakuwa da karin sabo da juna



2- yana sa tausayi da sanin halin da Partner ke ciki a cikin awoyin bacci.(incase daya daga cikinsu zai samu rashin Lafiya cikin dare, ko bad dream ko wani attack)




3 - Kwana waje daya da maigida zai sa kusan halin da yake ciki, haka kema zai San halin da kike ciki farin ciki ko akasi ko wata damuwa. Haka idan anyi fada fushi da juna ba zai dauki dogon lokaci ba za a fahimci juna.




Abubuwan da Ma'aurata zasu kiyaye;

Firan Dare

Mu Lura da wannan 'yan uwa Mata, hirar dare nasa maigida ya daina fita yawo da daddare, Saboda baya samun hirar dare daga gare ki, kuma galibi idan suka fita, sai sun raba dare ana tadi a waje, lokacin da zai dawo, ke Kuma sannan kinyi barci..Kinga irin wannan Ina amfaninsa.





Kin dinga jawo hankalin maigidanki, ta wannan sigar, domin ya kaucewa hanyar banza kamar zina, debo cuta, shan giya, abokan banza da sauransu.




A Kullum Bayan sallah Isha, idan aka ci abinci, sai a dasa hira, Har lokacin barci yayi, in ma mijinki baya so, to Yau da Kullum idan ya ga ki na yawan damunsa da hirar.





To zaki ga ya dawo yana so, muddin kika saba masa da wannan, ba zai dinga fita yawo ba, Amma idan kika yi sakaci ya saba da fita, to duk randa kika so ya bari, ba zai bari ba.





To duk wadannan abubuwan Zaki samu damar yin sune idan kuna kwana daki daya, saboda in raba daki kuke sai ya fice da dare ya tafi yawonsa, daga yawon fira wajen abokai shikenan zai samu gurbatattu daga ciki su koya mai yawon dare, da yin wasu abubuwa da bai kamata ba. Don haka sai a kiyaye.

Comments