Ingantattun Magunnan Gyaran Nono guda Hudu Da Yanda Ake Amfani Da Su
Idan muka ce gyaran nono akasari ba kowace mace zata gane me muke nufi ba saboda wasu basu damu da gyarawaba, alhali kuma rashin gyaran ba karamar illa yake yi ba amma su basu san hakan ba, to gaskiya yana da matukar muhimmanci da tasiri ga mace AMARYA ko UWARGIDA, BUDURWA KO ZAWARA, da ku gyara nononku.
Karki bar nononki haka nan sharaf ba kyan gani, sai kaga mace ta bar nono a zube, in tana shara mai gida yaga suna ta reto kamar an ratayo agwagi a bayan keke, gaskiya hakan zai iya rage maki tasiri wajen maigida, hanyoyin da zaki bi don kada nononki ya fadi ko kuma idan ya fadi kuma kina son ya tashi sune zaki samu:
- Alkama ki rinka yin kunu da ita kina sha safe da rana.
- Ko kisamu garin hulba da garin tsamiya da zuma farar saka da lemun tsami
Sai ki hadasu guri daya ki rinka shafawa a nonon, bayan awa daya ko ( 30 minutes) sai ki wanke ki shafa man zaitun,
malama zaki sha mamaki Insha Allah
Gyaran Nono Ga Budurwa
wannan wani hadi ne da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wannan hadi kuma kowace macema intana bukata zata iya amfani dashi saboda tasirinshi, yanda akeyi shine za a samu.
- Garin waken soya
- Garin alkama
- Garin zogale
- Garin bawon lemun zaki
- Kunfan maliya
- Zuma
Sai kicakudasu guri daya sai ki rinka shafawa a nonon bayan 30mtn ko sama da haka sai ki wanke,sannan kuma ki rinka shan kunun alkama zaki sha mamaki.
Don Dawo Da Martabar Nonoki
Ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko girmansa yanda zatayi shine zata samu ganyen sabara mai kyau da ‘ya’yan alkama suma masu kyau sai ki rinka kunu dasu, ko kunun gyada, ko kunun alkama, ko kunun shinkafa, ko kunun gero, ko koko duk dai wanda yasamu sai ki dafashi da wannan hadin mai albarka.
Allah Yasa adace Ameen
Comments
Post a Comment