Main menu

Pages

YADDA SAKACI ZAI IYA SA ABINCINMU SU ZAMA GUBA

 



Ko Kunsan Abincin Ku Zai Iya Zama Guba A Gareku?


Ku biyo mu kuji wannan baƙin dake bayan Albasa minene shi kuma mi yake iya haifarwa ga lafiyar ɗan Adam.


Wata ƙila zaku riƙa ganin shi a bayan Albasa amma baku taɓa kawo wa cewa yana da hatsari ba ga lafiyar ku.





Shi wannan baƙin abu da kuke gani cutace ta wasu ƙananan ƙwayoyin hallita da ake cema Fungi, sunan cutar da suke haifarwa kuma ana kiranta da ASPERGILLUS NIGER.


Haka kuma tana yaɗo akan wasu nau'in kayan abinci da suka haɗa da Albasa, Gyada da Grapes, haka kalar baƙin na da ɗabi'ar haifar da wani sinadarin da ake kira (Melanin) a bayan Albasar da ta bushe.





Shi dai wannan sinadarin idan aka shaka yana iya haifar da cutar huhu mai tsanani da ake kira ASPERGILLOSIS ( Sai dai ba'a cika samun ta ba ga Mutane waɗanda garkuwar jikin su take da ƙarfi) amma dai tana iya yin illah ga Mutanen da suke da ciwuka irin su Asthma, ciwon Sugar, cutar Huhu da kuma cutar ƙanjamau HIV, da sauran su.


Kazalika tana iya haddasa wata cuta da zata riƙa sanya ruwan kunnai da ake kira OTOMYCOSIS.





Bincike ya nuna cewa wasu daga cikin waɗannan ƙwayoyin cutar na Aspergillus Niger suna haddasa wata guba mai suna OCHRATOXIN wadda zata iya haifar da cutar Mafitsara, wani binciken ma ya nuna cewa zata iya haifar da cutar kansa.


Wata ƙwayar cutar mai hatsari kuma itace ASPERGILLUS FLAVUS, wadda ake samu ita kuma ga Tumatarin da ya lalace irin Wanda akafi sani da "Bage" Mutane da dama suna sayen shi saboda sauƙin da yake dashi.






Ita Aspergillus Flavus takan fitar da sinadarin guba mai suna Aflatoxin, ita kalar wannan gubar tana da wuyar narkarwa koda kuwa an sanyata a wuta bata cika mutuwa ba.


Kazalika Aflatoxins an sansu da haddasa cutar kansar hanta da kuma cutar Hepatitis, kuma tana rage garkuwar jikin Ɗan Adam.


 Wannan kaɗai ya isa yasa Mutane su daina sayen ruɓabɓen tumatar ko Albasa a kasuwa.

Comments