Yanda Ake sarrafa tumfafiya don magungunan Maza da Mata
Ana amfani da furen tumfafiya ga masu farfadiya da kuma ciwon kurkunu. Ana amfani da kunnuwan tumfafiya a maida basir mai tsiro. Za a nemi kunnuwan tumfafiya kamar kwara biyu ko uku haka sai a dan kara su ga zafin wuta kadan sai a danne dubura da su in sha Allahu nan take duburar za ta koma.
Ana tarfa ruwan tumfafiya kamar digo biyu a cikin kunnen dake ciwo za a yi haka sau daya zuwa biyu. Amma idan kunnen na ruwa to sai a tafasa itatuwan tumfafiyar misalin kofi daya sai a rinka wanke kunnen dake ciwo da su.
Tumfafiya na maganin dan kanoma wanda ya tsananta, shawara, ciwon ciki, yawan ciwon kai na ba gaira ba dalili, tarin nimoniya da kuma cutar kuturta.
Ana kona saiwar tumfafiya a maida su gari sai a hada da dan karamin cokali na garin lalle a daura a kan ciwon kafa ko hannu ko yatsan da ya kumbura ko ya ja ruwa kamar ciwon dan kankare ko wanda ake tunanin na kambun baka ne. Wannan kumshin zai zuke dafin ciwon a cikin karamin lokaci.
Ana amfani da tumfafiya a kona jinnun da aka turowa mutum ta hanyar sihiri. A nan za a nemi garin ganyen kaikayi koma kan mashekiya sai a nemi furen tumfafiya a shanya idan ya bushe sai a dake a gauraya su waje daya a nemi allo babba a rubuta abun da ya sauwaka daga ayoyin Alkur’ani mai girma sai a wanke a tafasa a sha tun da safe kamin a karya. Wallahi sihirin ko wane iri ne zai karye nan take cikin yardan Allah.
Ana zubar da ciki nan take lokacin da aka yi amfani da tumfafiya. Shima wannan ba zamu fadi yanda ake yin sa ba. Saboda lahaninsa da kuma damar da wasu za su samu ta aikata abin da bai dace ba.
Ana tafasa kunnuwan tumfafiya a dinga wanka da ruwan tun da safe dan maganin matsanancin ciwon gabobi da kuma jiyojin jiki.
Ana busar da furen tumfafiya sai a dake ya koma gari a rinka sha a cikin ruwan zafi duk lokacin da za a kwanta domin magance mutuwar gaba ga namiji.
Ana amfani da kunnuwan tumfafiya dan dawo da jinin al’adan daya dauke na tsawon lokaci. Ana turara kunnuwan tinfafiya dan warkar da asma da ciwon kai na gaban goshi.
A kan sanya ruwa a cikin kwallo 7 na diyan tumfafiya sai a bar ruwan sai sun kwana uku a ciki sai a juye ruwan a rubuta surar karfe a wanke a tarfa zuma cokali biyu a sha kamin a ci komai. Maganin sara na karfe kamar takobi ko wuka da rauni ko kariya mai tsanani ga jiki.
Ana amfani da ruwan tumfafiya wajen ciwon hakori. A nan ana diga ruwan tumfafiya a hakorin da ke ciwo.
Mata masu neman tagomashi ga mazajensu sai su nemi busashen garin tumfafiya sai su hada da garin lalle da kuma garin ganyen bishiyar birana. Sai dai kuma bishiyar tumfafiyar tana da ban tsoro musamman da dare inda takan canza bishiya ce da iskoki ke fakewa a gunta. Dan haka sai a san yanda aka tinkaren ta. Amma tana da fa’idodi da dama. Duk da yake ba kowane irin ilmi ya dace mu fayyace ba. Saboda fadar wani ilmi zai zamo illa. Da fatar duk abin da muka fada a kan kuskure za a gafarce mu kuma dan Allah duk wanda yakaranta ko yaturama yanuwa musulmi.
Comments
Post a Comment