Tasiri da Kuma Illar da Madara ke wa Mai fama da ciwon Ulcer.
Mutane da yawa suna shan madara walau na garinsa kona ruwa dazaran sunji alamomin olsarsu natashi musamman cikin watan azumi.
To Shan Madaran nada Fa'ida ga masu ciwon Ulcer?
Abunda yafi dacewa shine; Kafin ace nayi bayanin kaitsaye bari nakoma baya dan tunatarwa akan asalin abubuwan da suke janyo cutar olsa a jikin mutum.
Kunsan olsa itace wata gyambo datake samuwa acikin yankin farko na karamin hanji, wanda dagashi sai tumbi. Wani lokaci kuma gyanbon ana samun shine acikin tumbin. (On the duodenum or in the lining of stomach). Shi ake kira dasuna ulcer (kodai gyambon ciki a Hausance).
Olsa tana takurawa mutum sosai, musamman idan cikin mutum babu abinci.
Shidai madara zai taimakawa mai cutar olsa ne kawai saboda yana cika tumbi sannan sai mutum yaji olsar ta lafa amma nadan wani lokaci. Hakan bazaisa ace shan madara yanada kyau ko bashida kyau ga masu olsa ba. Adai ingantacciyar bincike da akeyi angano cewa abinci baya haddasa olsa kuma baya warkar da ita.
Yawancin kwayar cutar bakteriya maisuna Heliko bakta pailori (helicobacter pylori [H pylori]) dakuma yawan shan magangunan gajiya ko zafin ciwo misali kataflam da ciwotakwas su sukafi haddasawa mutum cutar ta olsa bawai abinci ba.
Abaya mutani dayawa sunyi amanna cewa madara yana maganin olsa, Wanda haryanzu wasu sunanan akan bakarsu.
Amman abun bahaka bane. Saboda yawan shan madaranma kara tsananta olsa yakeyi. Dalili kuwa shine :
Yana tsokano wani kwayar halitta maisuna parietal cells wanda yake acikin tumbin mutum. parietal cells kwayar halittane dayake samarda sinadarin acid maikona gyambon ciki idan yayi yawa (Zollinger-Ellison syndrome or hyperacidity). Shiyasa akejin wani zafi/kona alokacin da ake famada olsa. To kunji aikinda madara yakeyi kenan bayan yadan samarda sauki na dan lokaci.
Kenan Mai ciwon Ulcer zai daina Shan Madara ne
Amsar itace aah kuma eh
MADARA yana dauke da wasu sinadari masu amfani ajikin mutum, sinadarinda madara kedauke dasu sune: protein dakuma calcium. Amma protein dindake cikin madaran shike samarda sidarinda zai shawokan acid dindake cikin tumbi sannan kuma agefe guda yana tunzura kwayar halittar datake samarda sinadarin acid kaitsaye. Kenan za'a samu yawaitar acid bayaganan kuma asamu tsanantar ciwon. Idan har mai olsa zaisha madara, to lallai yasha Kadan bamai yawaba. Abunda yafi dacewa kuwa yakauracewa shanta kwata-kwata.
Idan kuma anyi gwaje-gwaje an gano cewa olsarka ba kwayar cutar bakteriya maisuna H.pylori bane ta janyo maka, kaitsaye zakasha madaranka. Amma kuma tareda magangunan dasuka dace.
Comments
Post a Comment