Main menu

Pages

AMFANIN DA GANYEN RAMA KE DASHI, DA YA KAMATA KOWA YA SANI

 



Amfanin dake tattare da cin Ganyen Rama da ba Kowa ya sani ba.

Ganyen rama wato ‘Jute Leaves’ ganye ne da mutane musamman na yankin arewacin Najeriya ke yawan amfani da ita.


Mutanen yankin arewacin Najeriya na yawan amfani da ita, inda takan zama abincin rana ko ta marmari.





Ana yin fate, dambu, a yi miyan ta zalla ko kuma a hada ta wajen yin miyan taushe, akan kuma dafata a kwada da kuli a ci.





Ga irin amfanin da ke tattare da cin ganyen rama:

1. Ganyen rama na dauke da sinadarin ‘Vitamin A,B,C,D da B-12 dake kara karfin ido, saurin nika abinci a ciki, sa jikin mutum warkewa musamman idan an sami rauni sannan ya na kara jini a jiki.



2. Ana samun sinadarin ‘Calcium’ wanda ke kara karfin kashi.



3. Yana dauke kuma da sinadarin Iron dake kara karfin kashi.



4. Rama na taimakawa wajen hana tsufa da wuri.



5. Yana taimakawa wajen wanke ciki.



6. Yana rage kiba a jiki.



7. Yana kawar da bugawar zuciya na farad daya.



8. Yana kawar da ciwon siga.


9. Ganyen rama na magani da kare mutum daga cutar sida ko kuma daji kowace iri.

Comments