Tasirin Amfani da man jirjeer guda goma ga Lafiyar Maza da Mata
Man Jirjeer (Cress Oil ko Rocket Oil) yana daga cikin nau'in magungunan da aka dade ana amfani dasu saboda muhimmancinsu da kuma amfaninsu.
Ga kadan daga cikin fa'idodinsa
1. Man Jirjeer yana Qara Qarfi ga Maza. Kamar mutumin da yake da Qaracin sha'awa, ko kuma rashin Qarfi, idan yana Shan Man Jirjeer acikin ruwan Lipton ba madara, insha Allahu za'a dace.
2. Yana sa Qarfin gashi ga Mata. Duk matar da take Shafa Man jirjeer, gashinta ba zai rika karkaryewa ba.
3. Wanda yake fama da matsalar Asma ko tari, idan yana shansa insha Allah zai samu waraka. Hakanan duk wani nau'in ciwon Qirji ko Majina, in sha Allahu idan anyi amfani dashi za'a dace.
4. Wanda yake da Qarancin Jini ajikinsa, idan yana shan Man jirjeer ko kuma Garinsa, zai samu Qaruwar jinin jikinsa.
5. Bincike ya nuna cewar Jirjeer yana kashe 97% na Kwayoyin chutar Daji. Musamman ma Sankaran Mama (Breast Cancer).
6. Matar da Jinin al'adarta ya rikice, idan tana amfani da Man Jirjeer zata samu waraka.
7. Mutumin da yake fama da Sickle cell Anaemia (Sikila) idan yana sha kuma yana shafa man Jirjeer za'a dace.
8. Matar da take shayarwa idan tana shan Man jirjeer zata samu Qaruwar ruwan nononta. Shi yasa ma akasashen da suke nomanta, da zarar mace ta haihu suke bata yawancin abincin da yake dauke da Ganyen Jirjeer acikinsa.
9. Likitocin Islama da dama sunyi magana akan Muhimmancinta tunda Manzo (saw) ma yayi magana akanta.
10. Mutumin da Cinnaka ko rina ko zuma ta harbeshi, idan ya shafa Man jirjeer nan take zai samu waraka.
NOTE: Matar da take dauke da Juna biyu kar tasha Man Jirjeer domin kuwa yana matsowa Wuyan mahaifarta kuma zai iya haddasa mata 'bari ko nakuda cikin gaggawa. Don haka akiyaye.
Comments
Post a Comment