Main menu

Pages

AMFANIN TAFARNUWA WAJEN INGANTA LAFIYA DA KARIYAR JIKIN MU

 



Amfanin Tafarnuwa wajen inganta kariyar jiki da Kara Lafiyar Dan Adam

A yau mun kawo maku amfanin tafarnuwa dan samun kariya daga wasu cutuka na kwayar cuta ta Viral, bacterial da kuma fungal da kuma baiwa jiki damar samun ingantattar lafiya (sound health).





Ita dai tafarnuwa an fara amfani da ita a yankin Asiya ta tsakiya kimanin shekarru dubu biyar zuwa shidda da suka gabata, haka kuma ana amfani da ita a bangaren abinci da kuma sarrafa magani (for diet and drugs).A yanzu ana amfani da ita a yankin gabas ta tsakiya da kuma Afirika da nahiyar turai.





Tafarnuwa nada dubban amfani wanda har zuwa yanzu ba a ida tantance dinbin amfaninta ba, duk da yake yawan cin tafarnuwa kan sa mutum ya rinka warinta a dan haka sai a rinka ci akan ka'ida.



Ana soya tafarnuwa tamkar yanda ake soya albasa sai a rinka tarfawa ga abinci ko nama ana ci.

Tafarnuwa tana magance mafi yawan cutukan fata(cures a number of skin disease) kamar irin kurajen fuska sai a rinka gogata akan fuska bayan an tsagata. Ana yin haka na tsawon sati daya.





Tana maganin ciwon tari kamar na bronchities da masu fama da ciwon sanyin kirji (chest infection)

Tana maganin sanyin mara da ciwon sanyin mata a sabili da jima'i da mai ciwon (gonorrhoea).tana kuma maganin karancin jini a saboda rashin cin abinci dan tana gyara miyau ta yanda hakan zai baiwa mutum damar cin abinci isasshe (appetite)





Tana karfafa garkuwan jiki dan yaki da cutuka da dama (immunity)

ana baiwa kananin yara ita dan tana ba jikinsu kwarin guiwa da kuma kare 'yan cutukan dake yiwa yara karan tsaye.





Bugu da kari tana maganin cutukan zuciya dan takan rage yawan barazanar sinadiran cholesterol.

Tana karfafa girman sababbin kwayoyin halitta (boosts the growth of new cells).


Comments