Amfanin yin Family Planning guda goma, da ire iren magungunan da ake amfani dasu
Tsarin iyali (Family Planning) hanya ce da ma’aurata kan yi amfani da ita wajen tsara wa junansu lokacin da ya kamata su fara haihuwa da kuma tazara tsakanin haihuwar.
Wasu daga cikin magungunan Family Planning da ake amfani dasu a Nigeria
1- Oral Pills
- Excluton
- Mycrogynon
2- Injectable
- Norist
- Depo
- Sayana.
3- Long term Method
- Implanon
- Jadelle
- IUCD
4- Barriar Method
- Male Condom
- Female Condom
- Diaphragm
Menene Amfanin family planning ?
Tabbas family planning yanada amfani sosai amma ga kadan daga cikin su :
1- Yana karawa Yaro/Yara annashuwa, sakamakon kulawar da suke samu daga wajen iyayensu.
2- Yana sa yara su samu kulawa ta ɓangaren lafiyarsu da kuma samun ingantaccen ilmi.
3- Mace za ta samu isasshiyar dama wajen cigaba da rayuwarta, sannan ta taimaka wajen bunƙasa cigaban iyalinta.
4- Mace za ta samu isasshen lokacin kula da mijinta da kuma samun ƙarin danƙon soyayya.
5- Yana rage damuwa da kasala ga mata a gidajensu.
6- Za tabawa mace damar shayar da jaririnta na tsawon lokaci, inda yin hakan kan ba da kariya daga cututtuka da dama.
7- Tazarar haihuwa kan baiwa Maigida damar kulawa da iyalansa yadda ya kamata.
8- Maigida yakan samu ƙarancin damuwa da kasala a rayuwarsa ta yau da gobe.
9- Haka nan zai samu isasshen lokacin zama da iyalinsa a gida da kuma ba su tarbiyyar da ta dace.
10- Zai ba wa Maigida damar sauke nauyin da ke kansa na tarbiyya da sauran haƙƙoƙin da ke wuyansa na rayuwar ‘ya’yansa.
Bayanin akan magungunan :
1. Oral Pills :
- Excluton: Na masu Shayarwa ne
- Myctogynon : ana iya bawa kowa idan babu wani dalili na contraindication.
-Oral Pills : kwayoyi na hadiya da ake sha, don dakatar da haihuwa har zuwa wani lokaci. Wadannan kwayoyi iri biyu ne: akwai wanda ake hada sinadarin estrogen da progestin a cikin kwaya daya (Myctogynon), akwai kuma wanda progestin din ne kadai a ciki (Excluton).
-Oral pills- akan shasu a kullun kwaya 1 idan kikasha idan kin sadu da minjinki Insha Allah ba Zaki samu ciki ba.
Zamu cigaba da bayanan a next post Insha Allah
Comments
Post a Comment