Rawar da yawaita Shan Kara/Rake ke takawa a ingancin Lafiyar Dan Adam
Rake wadda a Turance ake kira da sugar cane ana nomata a sassa daban daban a fadin duniya.
Bincike ya tabbatar da cewa kashi dari na ruwan rake natural ne da basa neman wani hadi ko karin wani sinadiri daga ilmin mutum(100% Natural drink )
Yana dauke da gram 30 na natural sugar. Bata da kitse ko misqala zarratin(zero contents of fat), haka kuma bata dauke da wani abu da ya shafi sinadirin cholesterol ko wani abinci mai tarawa mutum kitse ko haifar da tumbi da nauyin jiki. Sai dai tana dauke da sinadiran Calcium, sodium, potassium, magnesium da kuma Iron.
Dalilin rake na mallakar wadannan sinadirran masu amfanar jiki sai ince har maganin wasu cutukka take yi.
A duk sanda kake fama da jinya ko rashin karfin jiki a sanadin karancin ruwan jiki (dehydration) to sai ka yawaita shan rake. Hakan zai maida maka da ruwan jikinka da kuma baka qarfin jiki nan take (instant energy)
Rake tana fadada lafiyar hanta(enhances liver function) Natural treatment ce ga cutukkan hanta(liver related diseases)
Maganin ciwon shawara
(jaundice) A duk lokacin da kake tinanin kamar kana fama da ciwon shawara to akoi bukatar ka yawaita shan rake a hakika akoi fa 'ida domin zata warkar maka da wannan ciwon.
Rake na yaqar qwayoyin dake haddasa ciwon daji kamar cancer kenan. Domin tana daukeda dimbin sinadiran potassium,Iron da magnesium wadanda kan taru su koma alkaline in nature ta yanda zasu samarda flavonoids masu iya yaqi da cancer cells musamman masu haifarda prostaye da kansar mamma.
Tana saurin narkarda abinci mai qarfi da ya jima a ciki dan take zata jika hanji(ease digestion).Dan haka a duk sanda kaji cikinka ya kumbura ko ya qabe to ka nemi rake ka sha bayan minti ashirin zakaji cikin naka yana sacewa.
Rake na kawo natsuwa da daukar hankali.A duk sanda kaji jikinka ba dadi haka to sai ka nemi rake ka sha zata sakaka a cikin nishadi.
Rake na maganin cutukkan ciki (stomach infections ) kamar kumburin ciki,bushewar ciki dama jin tashin zuciya.sai a nemi rake mai zaqi a rinka sha akai akai.
Rake tana da zaqi kuma zaqinta baya haifarda ciwon suga.
Yawan sukarin dake gareta yana dasqare barazanar kamuwa da ciwon suga.
Tana inganta lafiyar qoda.(kidney health)
Tana rage radadin cutukkan dake da alaqa da fitsari ko wadanda ake dauka ta fannin saduwa.
Urinary tract infections and Sexually transmitted diseases.
Musamman idan an gaurayata da ruwan kwakakwa.
Tana taimakawa dan samuwar karfin k'ashi da karfin haqora (bones and teeth)
tana kare rubewar haqora.(tooth decay.
Idan dukkanin kayan zaqi na cuturwa amma banda zaqin rake dana tsirran itatuwa.Natural fruits ne da ke daukeda dimbin sinadiran dake amfanar jiki(essential vitamins).
Comments
Post a Comment