Main menu

Pages

BAYANI AKAN SINADARIN DA KE KAWO HAWAN JINI, SUGAR DA ZUCIYA

 



Sunadarin da ke haddasa hawan jini, sugar da ciwon zuciya.

Wannan ba wani abu ba ne face sinadarin "Cholesterol"

Cholesterol sinadari ne mai danko kamar kitse, kuma yana da amfani ajikin Dan Adam sannan idan yayi yawa yana cutarwa kwarai da gaske.





Insha Allahu zan fada muku Kadan daga cikin Amfaninsa sannan inyi muku bayani akan Illarsa, da abubuwan da yake yawaita shi ajikin mutum, da kuma abin da yake rage shi.



Amfanin Cholesterol

1- Yana daidaita Sukari da Jinin mutum.


2- Yana samar da sinadari mai saka kwarin kashi da kwarin Hakori wato, Vitamin D.


3- Yana ba mutum kariya daga kamuwa da cututtuka kamar su: Virus, Infection funglas....


Kowane abu ya kan zama mai amfani ta wani bangaren, sannan ya cutar ta wani wajen.





Illolin Cholesterol a jikin Dan Adam

1- Idan Cholesterol yayi yawa a jikin mutum yana haddasa toshewar jijiyoyi wato fayif din hanyoyin jininsa. "Plague/atherosclerosis"


 Daga nan sai hanyoyin da ke kawo jini zuwa zuciya su toshe, wato coronary artery disease" daga nan sai Zuciya ta kasa harba jini zuwa sauran hanyoyin jini, wato "Heard failure"


2- Yana sa Hawan jini.


3- Yana saka Ciwon suga.


4- Mutuwar barin jiki, Paralyse.


5- Yana hana na mijin Ya sadu da matarsa, "Free mature ejaculation".




Abubuwan da suke kawo yawaitar Cholesterol a jikin Dan Adam

1- Yawan cin "lipo protein", kamar su nama, Kwai... 


2- Yawan cin kayan "poultry" kamar su Kajin Gidan goma, kwan gidan gona, Kifin gidan goma.... 


3- Yawan cin "saturated fatty acid" kamar Madara, chocolate, Butter.... 


4- Yawan cin kayan gwangwani "can food" kamar su: kifin gwangwamani, lemon Gwangwani.... 


5- Kwanciya bayan anci Abinci, kafin abinci ya narke.


6- Yawan Cin abu mai kitse "FAT"





Hanyoyin da za a bi don rage cholesterol a jikin Mutum

1- Yawan cin kayan ganye da Kuma 'Ya'yan itatuwa. 


2- Yawan motsa jiki. (Yawan Sallar Nafila) 


3- Yawan saka lemon tsami cikin abinci.

Comments