Dalilin da ya sa na daina rubuta fim ɗin Labarina - Ibrahim Birniwa
An fara haska fim ɗin Labarina a watan Yulin 2020, wanda kamfanin Saira Movies ke shiryawa
Shahararren marubucin fina-finan Kannywood Ibrahim Birniwa ya ce ya daina rubuta fitaccen fim ɗin Labarina mai dogon zango saboda rashin jituwa tsakaninsa da masu shirya shi da kuma aiki kan nasa fim ɗin.
Duk da cewa rashin jituwa ce ta sa marubucin ya fita daga fim ɗin, sai dai ya ƙi faɗa wa BBC Hausa ainahin abin da ya faru, yana mai cewa "da ni nake rubuta fim ɗin da zuwa yanzu ya zo ƙarshe".
Da yake magana ta cikin shirin Amsoshin Takardunku na Sashen Hausa na BBC a ƙarshen mako, Birniwa ya ce ba zai yiwu ya koma rubuta labarin fim ɗin ba a nan gaba saboda wasu dalilai.
Ga masu bibiyar fim ɗin na Labarina, za su lura da daina ganin sunan Ibrahim Birniwa a cikin marubutansa, inda Nasiru Gwangwazo da Yakubu M. Kumo da Saddika Yahaya da Maimuna Beli suka maye gurbin sa.
Birniwa ya ce duk da ba salin-alin suka rabu da mashiryan Labarina ba, wanda Aminu Saira ke ba da umarni, amma dai ba baram-baram suka rabu ba kamar taurarin fim ɗin Nafisa Abdullahi (Sumayya) da Nuhu Abdullahi (Mahmud).
"Kafin fim ɗin Labarina, mun yi ayyuka da dama da Aminu Saira, wasu manyan fina-finai da ya ba da umarninsu, ni ne na rubuta su, saboda haka muna da alaƙar da ba za a yi baram-baram ba," in ji shi.
"Abin da ya faru bai kai a kira shi baram-baram ba duk da cewa ba haka aka so ba. Kamar yadda na faɗa, akwai ayyukana da na saka a gaba."
Da ni nake rubuta fim ɗin da tuni ya zo ƙarshe
Yanzu haka fim ɗin Labarina da ake haskawa a tashar Saira Movies ta dandalin YouTube da kuma tashar talabijin ta Arewa 24 na zango na biyar bayan fara haska shi a watan Yulin 2020.
Ibrahim Birniwa ne marubucin fim ɗin har zuwa tsakiyar zango na uku, kamar yadda ya faɗa wa BBC.
Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar ya ci gaba da rubuta fim ɗin, ya amsa da cewa: "Ko da akwai yiwuwar dawowar ma zan ce maka a'a, saboda da ni nake rubuta labarin da na kai shi wajen da ya kamata a ce ya ƙare.
"Sannan ko su da suke rubutawa ma ina tsammanin sun zo ƙarshe. Wataƙila sun gama rubuta labarin daga nan har zuwa ƙarshe."
BBC ta tuntuɓi Aminu Saira game da zargin amma ya ce "ba na son saka baki a irin waɗannan maganganun, ba zan ce komai ba".
Birniwa ya ce aikin da ya sa a gaba shi ne na 'Matasa Games' da ake haskawa a gidan talabijin na Arewa 24, wanda ya ce "yanzu ma aka fara haska shi".
Comments
Post a Comment