Yanda za a hada maganin ciwon kunne a samu waraka cikin yaddar Allah
Ayau mun kawo muku yadda za a magance matsalar ciwon kunne insha Allahu.
Yawanci ciwom kunne ya fi matsawa mutum lokacin sanyi ko damuna, amma idan kasan kana yawan yin ciwon kunne ko hakori ko ciwon ido, to ka rika ta'ammali da maganin sanyi, insha Allah zaka ga abun yana rabuwa dakai.
Game da maganin ciwon kunnen abun da zaka nema sune kamar haka.
1. Man zaitun
2. Man Tafarnuwa
Yadda Za a Hada;
Da farko zaka samu auduga ka goge kunnen naka sosai, sai ka hada chokali biyu na man tafarnuwa da chokali daya na man zaitun, za a rika diga digo uku a kunnen da yake ciwo ko kaikayi ko yawan kuka da dare kafin kwanciya, asa auduga a toshe zuwa safiya a cire a sake goge kunnen.
.Note; sai dai wajen give kunnen ayi a hankali Kuma sama sama kar a goge har ciki wajen dodon kunne, in ana yawan tabi dodon kunne akwai babbar matsala.
Haka za'ai har a samu waraka.
Comments
Post a Comment